Cutar Murar Tsuntsaye
Cutar Murar Aladu ita dai murar aladu da aka yiwa laƙabi da H1N1 an fara samun ɓullar ta ne a ƙasar Mexico da kuma Amurka a ranakun 23 da 24 ga watan afirilun shekara ta 2009. Hukumomin lafiya a Mexico ne suka fara bada rahoton mutanen da suka kamu da wannan cuta, wanda kafin kace kwabo kimanin mutane 854 sun kamu da alamun wannan cuta. Bayan gwaje-gwaje da bincike irin na likitoci daga bisani dai mutane a kalla 59 ne suka rasu a Mexico a cikin yan kwanaki ƙalilan. lamarin da ala tilas ya zamewa jami'an gwamnatin Mexico saka dokar hana yawo a biranen ƙasar domin tsagaita yaɗuwar cutar. Amma wannan mataki bai hana cutar bazuwa zuwa wasu ƙasashen duniya ba, musan man ƙasar Amurka da Canada da al'umomin su ke yawan zirga-zirga tsakanin ƙasashen juna.
| |
Iri |
influenza pandemic (en) public health emergency of international concern (en) Annoba |
---|---|
Kwanan watan | ga Maris, 2009 – 10 ga Augusta, 2010 |
Wuri | worldwide (en) |
Ƙasa | Tarayyar Amurka da Central Mexico (en) |
Sanadi | pandemic H1N1/09 virus (en) |
Adadin waɗanda suka rasu | 284,000 |
Wannan mukalar bata da Reference (Manazarta) ko daya, ka taimaka ta hanyar samar da Manazarta daga littafi ko yanar gizo, duba wannan shafin domin samun masaniya akan yanda zaka samar da Reference (Manazarta) a cikin wannan mukalar.
. |
Kokarin Kare Yaduwarta
gyara sasheKuma ganin yadda wannan cuta ke yaɗuwa kamar wutar daji yasa hukumar lafiya ta duniya WHO ta bayyana wannan cuta a matsayin annoba a duniya. Domin kuwa bayan wa'yancan ƙasashe na Amurka, sai cutar ta fara bazuwa zuwa sauran ƙasashen duniya daban-daban. Ƙarshen ta ƙaitawa dai daga watan na afirilu zuwa wannan lokaci cutar ta bazu zuwa ƙasashen duniya 206 ciki kuwa harda Najeriya da wasu ƙasashen afirka irin su Ghana da Afirka ta Kudu da Masar. A wata ƙididdiga da hukumar lafiya ta duniya WHO ta fitar ya nuna cewar aƙalla ba'a ƙasara ba, mutane fiye da dubu biyu ne suka rasu.
Yadda cutar take
gyara sasheAmma don gane da batun alamomi da banbancin cutar ta H1N1 da murar da aka sani ta sanyi da kuma murar tsuntsaye kuwa likitoci sun ce "wannan cutar ta murar aladun ana kamuwa da ita ne daga aladu kana daga bisani mutane suka fara kamuwa da ita. lamarin daya sa tafi ƙarfin duk wasu magunguna da aka sani dake maganin cutar murrar lokacin sanyi, ko bil'adama. Kuma banbancin ta da murar tsuntsaye shine kasancewar, ita murar aladu ta samo asali ne daga aladu, a yayinda murar tsuntsaye keda nasaba da tsuntsaye." Kuma alamun ta shine zazzaɓi mai zafi.