Christopher Odetunde
Christopher Odetunde, farfesa ne a fannin injiniyan jiragen sama da Mechanical Engineering. Ya riƙe muƙamai daban-daban a masana'antu da makarantu yayin da yake Amurka da kuma a Najeriya. Shi ne tsohon shugaban tsangayar Injiniyanci a Jami’ar Jihar Kwara, Malete[1] kuma Mataimakin Shugaban Jami’ar Augustine na yanzu.[2]
Christopher Odetunde | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | Kwara, |
ƙasa | Najeriya |
Karatu | |
Makaranta |
Embry–Riddle Aeronautical University, Daytona Beach (en) Iowa State University (en) Texas A&M University (en) |
Harsuna |
Turanci Pidgin na Najeriya |
Sana'a | |
Sana'a | Malami |
Ilimi
gyara sasheOdetunde ya yi karatunsa na sakandare a St. John's College Kaduna daga shekarun 1964 zuwa 1968, inda ya karanci fannin fasaha. Canjin sa zuwa fannonin kimiyya ya zo ne a matakinsa na A, wanda ya wuce tsakanin shekarun 1969 zuwa 1972.
Daga nan ya ci gaba da karatun Injiniyanci a fannin Aeronautical a Jami'ar Embry-Riddle Aeronautical dake Amurka. Ya sami wasu digiri a Jami'ar Jihar Iowa, Jami'ar Texas A&M da Cibiyar Fasaha ta Kudu maso Gabas, Alabama. Yana da Digiri na Dakta na Kimiyya a Injiniyancin Aeronautical, Master of science a Injiniyancin Aeronautical/Mechanical da Gudanar da Ayyuka, haka kuma da Digiri na Dakta a fannin Injiniyanci na Aerospace.[3]
Sana'a
gyara sasheOdetunde ya zama Mataimakin Shugaban Jami'ar Augustine a ranar 5 ga watan Oktoba 2020. Har zuwa lokacin da aka naɗa shi, ya kasance tsohon shugaban tsangayar Injiniyanci a Jami’ar Jihar Kwara, Malete.[4][5][6][7]
Manazarta
gyara sashe- ↑ "Kwara State University – University for Community Development". Archived from the original on 9 December 2022. Retrieved 3 March 2022.
- ↑ "Augustine University Ilara Epe: History". augustineuniversity.edu.ng.
- ↑ https://nuc.edu.ng/wp-content/uploads/2019/02/Directory-of-Full-Professors-in-the-Nigerian-University-System.pdf Samfuri:Bare URL PDF
- ↑ "VC canvasses holistic education system for national devt". 16 December 2021. Archived from the original on 3 November 2023. Retrieved 31 December 2023.
- ↑ "Augustine University Ilara Epe:News". augustineuniversity.edu.ng.
- ↑ "All You Need To Know About Augustine University - Vice Chancellor" – via www.youtube.com.
- ↑ "Igbomina Professor, Bode Odetunde appointed Vice Chancellor in Lagos". 18 September 2020. Archived from the original on 15 August 2022. Retrieved 31 December 2023.