Chris Ihidero (an haife shi ranar 19 ga watan Maris, 1976) ɗan fim ne na ƙasar Najeriya. Shi ne babban marubuci / editan labari a wasan kwaikwayo na TV na MNet Hush.[1]

Tarihin rayuwa gyara sashe

Ihidero na da digiri na farko da na biyu a fannin wallafe-wallafen Ingilishi daga Jami'ar Jihar Legas da Jami'ar Ibadan.

Ya yi aiki a matsayin mai zane-zane na gidan wasan kwaikwayo, mai watsa shirye-shirye, marubucin jarida, editan mujalla kuma malamin Jami'a. Daga shekara ta 2005, ya koyar a Makarantar Nazarin Lokaci na Jami'ar Jihar Legas.

Ayyukan fim / Daraktan fim gyara sashe

Ihidero ya ba da umarni sama da sa'o'i 100 na wasan kwaikwayo na shirin talabijin mai dogon zango. Ya yi gajeren fina-finai guda biyu, ciki har da Big Daddy (2012), wani fim game da fyaɗe, wanda aka fara a Silverbird Cinemas a Legas a watan Disamba na shekara ta 2011. Shirin ya sami sama da makallata 500,000, ya zama gajeren fim da aka fi kallo a Najeriya. Fim ɗin lashe kyautar "Special Jury Award" da "Best Editing Award" a bikin fina-finai na ƙasa da ƙasa na 2012 In-Short wanda ya faru a Legas a watan Oktoba na shekara ta 2012.

Fina-finai gyara sashe

  • Fuji House of Commotion – Director, over 52 episodes, Television Comedy, since September 2008
  • Now We Are Married – Director, Television Drama, 18 episodes, 2009/2012.
  • VIP – Director, 15 episodes, Television Thriller, 2010
  • Big Daddy, Writer-Director-Producer, Short Film (12Mins). 2011.
  • It Happened to Me – Director. Short Film (15mins). 2013.
  • Shuga – Producer. 2014.
  • HUSH – MNET Series. – Head Writer/Story Editor
  • FORBIDDEN – MNET Series. -Head Writer/ Showrunner

Manazarta gyara sashe

  1. "CPA Interview – Chris Ihidero talks movies, TV and cinema in Nigeria". CPAfrica. 7 March 2017. Archived from the original on 17 January 2018. Retrieved 16 January 2018.