Chinaza Uchendu

Dan wasan kwallon ne a Najeriya

Chinaza Love Uchendu (an haife tane a 3 ga watan Disamban 1997) itace yar wasan ƙwallon ƙafa ta ƙasa da ƙasa ta Nijeriya da ke buga musu atakin (gaba) . Ta kasance mamba a kungiyar kwallon kafa ta mata ta Najeriya . A matakin kungiyar ta buga wa kungiyar kwallon kafa ta Rivers Angels kafin ta koma Braga da ke Portugal .

Chinaza Uchendu
Rayuwa
Haihuwa Lagos, 3 Disamba 1997 (26 shekaru)
ƙasa Najeriya
Harshen uwa Harshen Ibo
Karatu
Harsuna Turanci
Harshen Ibo
Pidgin na Najeriya
Sana'a
Sana'a ɗan wasan ƙwallon ƙafa
Hanya
Ƙungiyoyi Shekaru Wasanni da ya/ta buga Ƙwallaye
Nasarawa Amazons (en) Fassara-2017
  Nigeria women's national under-20 football team (en) Fassara2015-2016
  Kungiyar kwallon kafa ta mata ta Najeriya2015-
Rivers Angels F.C. (en) Fassara2017-2018
SC Braga (en) Fassara2018-
 
Muƙami ko ƙwarewa Mai buga tsakiya

Wasan kwallon kafa gyara sashe

Uchendu ta taka leda a kungiyar kwallon kafa ta Rivers Angels a gasar Firimiya ta Mata ta Najeriya daga farkon shekarar 2017 har zuwa Yulin 2018 bayan hakan ta koma tare da taimakon zuwa Braga da ke kasar Portugal .[1]

Ayyukan duniya gyara sashe

A lokacin gasar cin kofin kasashen Afirka ta mata 2018 Uchendu ce kawai ta buga wasan karshe, inda aka shawo kanta a cikin mintuna 8 kafin karshen karin lokacin. Ta ci daya daga cikin fanareti hudu a bugun fenariti wanda ya kawo wa kungiyar kwallon kafa ta mata ta Najeriya gasar.[2]

Manazarta gyara sashe

  1. "Super Falcon star Uchendu joins Braga from Rivers Angels". The Cable News. 26 July 2018. Retrieved 22 December 2018.
  2. "Nigeria Women vs South Africa Women". CAF Online. 1 December 2018. Retrieved 22 December 2018.

Hanyoyin haɗin waje gyara sashe

  • Chinaza Uchendu
  • Bayani a SC Braga (in Portuguese)