Bello Sisqo
Bello Abubakar Sheriff, (Haihuwa: A ranar 1 ga watan Nuwamba, shekara ta 1998, wanda aka fi sani a masana'antar nishaɗi da suna Bello Sisqo, mawaƙin Jamus ne dan asalin Najeriya, mawaƙi ne, mai rawa ne, marubucin waƙa ne, kuma darektan kiɗa.[1][2]
Bello Sisqo | |
---|---|
Bello Abubakar Shariff | |
Haihuwa |
Bama Jihar Borno | Nuwamba 1, 1998
Gurin zama | Kasar Jamus |
Kasar asali | Najeriya |
Aiki |
|
Shekaran tashe | 2017–present |
Notable work |
|
Iyayes |
Abubakar Shariff (father) Hajiya Aisha (mother) |
Lamban girma | Best Artiste in Northern Nigeria Award|Best Music Video of the Year Award in 2021|Best EU Artiste Award |
Dan asalin karamar hukumar Bama dake a garin maiduguri, Najeriya. wanda ya girma a hanin kakarsa daga bisani ya koma gurin mahaifansa dake Miduguri.
Rayuwa
gyara sasheBello ya kasan ce maraya, an haife shi a ƙaramar hukumar Bama a jihar Borno. Mahaifin sa Abubakar Shariff da Hajiya Aisha Mahaifiyarsa, sun Rasu tun yana karamin yaro, hakan yasa Bello ya taso a jihar Kano tare da kakarsa yana da shekara 4, amma ya koma gurin mahaifinsa yayin da kakarsa ta Rasu, inda ya halarci makarantun gargajiya da na islamiyya kafin ya shiga harkar nishaɗi a garin maiduguri.
Tun yana ƙarami, Bello dan rawa ne ya fara koyar da rawa a Sinimar Farida da ke Rijiyar Lemo a Kano, yayin da Abokan sa na makaranta suke gayyatar sa don ya nishaɗantar da Jama'a lokacin yana dan shekara 9, Daga baya ya zama me horar da rawa a Kannywood inda ya koyar da galiban jarumai irin su fina-finan Ali Nuhu da Adam A Zango. Daga bisani ya cigaba da haɓɓaka fasahar waƙar sa.[3] Wanda a halin da yake ciki yakasan ce shahararren me Nishaɗantarwa ne da horar da waka da raye-raye.
Waka
gyara sasheDaga baya ya haɗu da wani shahararren mawaƙin Najeriya wanda ake kira da suna Chizo Germany, mai tasiri a shafukan sada zumunta a shekarar 2015 wanda shi ma ɗan Arewacin Najeriya ne. Sun haɗa kai don yin waka mai suna “Fada Da Gaskiya”. Wakar ce ta haskaka shi har ta kai ga hasashe. Da taimakon Chizo Germany, Bello ya sami zuwa Jamus inda ya ci gaba da harkokin nishaɗantarwa.[4][5]
Ya samu aikin horar da raye-raye inda ya horar da matakan raye-rayen gargajiya na Hausa da sauran al’adun Afirka.
Ya yi wakoki tare da Ice Prince, Jaywillz, Singah, Dijah, Zinolisky, da sauran manyan mawaƙan Najeriya. Ya kuma yi wakoki tare da mawakan Turai irinsu Gambiya, Jizzle da Chiara Damico. A Afirka ya yi waka tare da Macvoice daga Tanzaniya. Ya kuma yi Waƙoƙi da dama da mawakan Arewacin Najeriya kamar Adam Zango, Hamisu Breaker, Ado Gwanja, Ali Jita, Umar M Sharif, DJ Ab, Deezell, Sojaboy, Auta Mg Boy, Chizo 1 Germany, Classiq da Ahmad Shanawa.[6]
Darajoji[7]
gyara sashe- Kyautar Gwarzon Mawaƙa a Arewacin Najeriya
- Kyautar Bidiyo da Kiɗa na shekarar 2021
- Mafi kyawun Kyautar Mawaƙi na EU
Manazarta
gyara sashe- ↑ "Why Germans, Europeans love my Afrobeat songs – Singer, Bello Sisqo". Vanguard. Retrieved 9 January 2024.
- ↑ "Nigerian entertainment industry needs more funding – Bello Sisqo - SolaceBase". 27 January 2023. Retrieved 9 January 2024.
- ↑ Ibeh, Ifeanyi (2 January 2024). "Bello Sisqo's Afrobeats Hits Find Resonance in Germany's Music Scene". The Guardian Nigeria News - Nigeria and World News. Retrieved 9 January 2024.
- ↑ Nyamwaya, Rading' (28 September 2023). "Bello Sisqo to stun guests with performance at AFRONEWS Awards 2023 Gala Night". Afronews Germany. Retrieved 9 January 2024.
- ↑ Tracker, Nigerian (9 January 2023). "Why Nigerian entertainment industry needs more encouragement – Bello Sisqo". Nigerian Tracker. Retrieved 9 January 2024.
- ↑ "Nigerian entertainment industry is the fastest globally — Bello Sisqo". Daily Trust. 7 January 2023. Retrieved 9 January 2024.
- ↑ https://guardian.ng/saturday-magazine/bello-sisqos-afrobeats-hits-find-resonance-in-germanys-music-scene/