Ayo Omidiran
Ayo Hulayat Omidiran, (An haife ta ranar 10 ga watan Nuwamban, 1965). 'yar siyasan Najeriya ce kuma 'yar majalisar tarayya mai wakiltar mazabar tarayya ta Ayedaade/Irewole/Isokan na jihar Osun. Ita memba ce ta jam'iyyar All Progressive Congress. Ta kasance ‘yar asalin Ikire ce a cikin karamar hukumar Irewole ta jihar Osun.[1]
Ayo Omidiran | |||
---|---|---|---|
| |||
Rayuwa | |||
Haihuwa | 10 Nuwamba, 1963 (61 shekaru) | ||
ƙasa | Najeriya | ||
Harshen uwa | Yarbanci | ||
Karatu | |||
Makaranta | Jami'ar Ahmadu Bello Digiri a kimiyya : Biochemistry | ||
Harsuna |
Turanci Yarbanci Pidgin na Najeriya | ||
Sana'a | |||
Sana'a | ɗan siyasa da legislator (en) | ||
Imani | |||
Jam'iyar siyasa | All People's Congress (en) |
Ilimi
gyara sasheTa halarci makarantar Ayedaade Grammar School Ikire, a jihar Osun sannan ta samu takardar shedar kammala karatun ta na yankin Afirka ta Yamma (WAEC) a 1980. Daga nan ta wuce Jami’ar Ahmadu Bello zaria sannan ta kammala karatun digiri na farko a fannin Biochemistry a shekarar 1985.
Ayyuka
gyara sasheSiyasa
gyara sasheTa tsaya takarar majalisar wakilai ta tarayya mai wakiltar mazabar tarayya ta Ayedaade / Irewole / Isokan a shekarar 2011 kuma tayi nasarar lashe zaben. Ta sake tsayawa takara a shekara ta 2015 kuma an sake zaben ta a karkashin inuwar jam’iyyar APC. Ta rike mukamai da dama a majalisa ciki har da Mataimakiyar Shugaban, Kwamitin Majalisar kan Wasanni; memba na Kwamitin Majalisar kan Shari'a, Sadarwa, Cikin Gida, Abubuwan Ma'adanai Masu Kauri, Harkokin Mata da Mata a Majalisar.[2]
Gudanar da Wasanni
gyara sasheA shekarar 2002, ta zama memba a Hukumar Kwallon Kafa ta Najeriya kuma ta ci gaba da zama a can har zuwa 2005. Tun daga 2006, ta kasance mamba a kwamitin mata na FIFA . Ta zama mai mallakar Omidiran Babe, wata kungiyar kwallon kafa ta mata a Osogbo, jihar Osun a shekarar 1997. A 2017, an nada ta shugabar Hukumar Kwallon Kafa ta Mata ta NFF (NFF).[3]
Rayuwa
gyara sasheTa kasance mai sha'awar kwallon kafa. Ta dauki nauyin gasar Kwallan Kafa ta Mazabar Tarayya ta Ayedaade-Irewole-Isokan a farkon shekarar 2018 wacce ta kammala da wasan karshe a Ayedaade High School, Ikire, Jihar Osun.[4]
Manazarta
gyara sashe- ↑ "Hon (Mrs) Ayo Omidiran - The Official Website Of The State Of Osun". Archived from the originalon 2018-07-09. Retrieved 2018-07-03.
- ↑ "National Assembly | Federal Republic of Nigeria". Nass.gov.ng. Archived from the original on 2018-07-03. Retrieved 2018-07-03.
- ↑ "Akpodonor, Gowon (7 November 2017). "Omidiran's return will stabilize Nigerian women football, says Mabo". Retrieved 3 July 2018.
- ↑ Anonymous (29 March 2018). "Omidiran football fiesta thrills Osun community". The Guardian Nigeria (online). Retrieved 3 July 2018.