Ambaliyar Ruwa a Jihar Borno 2024

Ambaliyar ruwa ta 2024 a jihar Borno a watan Satumbar 2024 a Maiduguri da Jere, karamar hukumar Najeriya a jihar Borno, Najeriya. Ya raba sama da kashi 70% na mazauna jihar Borno sannan sama da kashi 70% na garin Maiduguri abin ya shafa a cewar Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA). [1] [2]

Ambaliyar Ruwa a Jihar Borno 2024
ambaliya
Bayanai
Ƙasa Najeriya
Kwanan wata Satumba 2024
Lokacin farawa 10 Satumba 2024
Wuri
Map
 11°50′27″N 13°07′55″E / 11.8409°N 13.1318795°E / 11.8409; 13.1318795
Ƴantacciyar ƙasaNajeriya
JihaJihar Borno
Sanda Kyarimi Park Zoo Entry Gate

Ci gaba da samun ruwan sama a garin Bama na Najeriya Damboa da karamar hukumar Gwoza ya janyo rugujewar madatsar ruwa ta Alau dake karamar hukumar Konduga wadda aka gina a shekarar 1984-1986. Rugujewar dam din ya haifar da ambaliya a jihar wanda ya kai ga nutsewar wasu kananan hukumomin da aka samu a kananan filaye a jihar.[3]

Gwamnan jihar, Farfesa Babagana Umara Zulum a cikin gaggawar mayar da martani ga ambaliyar ya bude sansanin ‘yan gudun hijira na Bakassi baya ga sauran sansanonin ‘yan gudun hijirar da ke yankunan tudu domin kula da lafiyar ‘yan kasa. Ya tabbatarwa da manema labarai cewa sama da mutane miliyan daya ne ambaliyar ta shafa a jihar.[4]

Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya ziyarci jihar domin ganin irin barnar da aka yi, ya kuma bada tabbacin taimakon gwamnatin tarayya da ta taimaka masu wajen shawo kan lamarin.[5]

Tasiri kan sauyin yanayi

gyara sashe

Gwamnan ya sanar da rufe makarantu a jihar sakamakon yadda ruwa ke ta karuwa sakamakon rugujewar dam din. Ambaliyar ta shafi gidan namun daji na Sanda Kyarimi, lambun dabbobi da wurin namun daji a Maidugiri. Rahoton ya nuna cewa dabbobi sun rasa rayukansu kuma mazauna yankin na cikin hadarin kai hari daga dabbobin.[6]

Babban asibitin jihar da kuma asibitin koyarwa na jami'ar Maiduguri suma sun sami matsala sakamakon ambaliyar ruwa. Haka kuma sansanonin ‘yan gudun hijira (IDP) ya shafa yayin da aka kwashe mutane daga sansanin El Miskin zuwa sansanin Bakasi domin tsira da rayukansu a cewar Darakta Janar na NEMA.[6] [7]

Haka kuma an samu labarin fashewar gidan yari sakamakon rugujewar gidan gyaran hali da ke Maiduguri sakamakon karuwar ambaliyar ruwa a jihar. Kakakin rundunar ‘yan sandan Najeriya reshen jihar Borno ya tabbatar da hakan. [8]

Ba iya wannan ba, ana rade-radin cewa gidan ajiyan namun daji, wato Zoo shi ma ya fashe. Hakan ya janyo aķe janyo hankalin al'umma da su kasance a ankare domin ba a san ina ne ruwan ya yada su ba.

 
Sarkin Potiskum tare da Gwamnan Jihar Borno Babagana Umara Zulum
 
Sarkin Borno His Royal Highness Alhaji (Dr) Abubakar Ibn Umar Garbai Al'amin EL-kanemi, Shehu of Borno, tare da Sarkin Potiskum His Royal Highness Mai Umar Ibn Wuriwa Bauya Lai-La.
  1. "Nigeria: Floods – Maiduguri (MMC) and Jere Floods Flash Update 1 (10 September 2024) - Nigeria | ReliefWeb". reliefweb.int (in Turanci). 2024-09-10. Retrieved 2024-09-11.
  2. Chibundu, Janefrances (2024-09-10). "REWIND: In 1994, Alau Dam collapsed, displacing 400,000 persons in Maiduguri". TheCable (in Turanci). Retrieved 2024-09-11.
  3. "Tinubu Rises to Maiduguri Flood Disaster, Promises to Assist State, Orders Evacuation – THISDAYLIVE". www.thisdaylive.com. Retrieved 2024-09-11.
  4. "Maiduguri Flood: One million people affected - Zulum - Daily Trust". Dailytrust (in Turanci). 2024-09-11. Retrieved 2024-09-11.
  5. Reporters, Our (2024-09-11). "Borno dam collapse: FG opens IDP camps as flood submerges 70% of Maiduguri". Punch Newspapers (in Turanci). Retrieved 2024-09-11.
  6. 6.0 6.1 Reporters, Our (2024-09-11). "Borno dam collapse: FG opens IDP camps as flood submerges 70% of Maiduguri". Punch Newspapers (in Turanci). Retrieved 2024-09-11.
  7. Pai, Bilkisu Halilu (2024-09-11). "NEMA deploys additional resources to rescue Maiduguri flood victims". Voice of Nigeria (in Turanci). Retrieved 2024-09-11.[permanent dead link]
  8. Reporters, Our (2024-09-11). "Borno dam collapse: FG opens IDP camps as flood submerges 70% of Maiduguri". Punch Newspapers (in Turanci). Retrieved 2024-09-11.