Aliyu Sabi Abdullahi

Dan siyasar Najeriya

Aliyu Sabi Abdullahi CON (an haife shi a ranar 10 ga watan Janairun shekara ta 1967) ɗan siyasar Najeriya ne, kuma Sanata mai wakiltar Neja ta Arewa a Majalisar Dattawan Jihar Neja a Majalisar Dokoki[1] ta Najeriya ta 8 da Majalisar Dokoki ta 9.[2][3][4] Shi ne mataimakin shugaban bulala a majalisar dokokin Najeriya ta tara.[5][6]

Aliyu Sabi Abdullahi
mamba a majalisar dattijai ta Najeriya

11 ga Yuni, 2019 -
District: Gundumar Sanatan Neja ta Arewa
mamba a majalisar dattijai ta Najeriya

6 ga Yuni, 2015 -
District: Gundumar Sanatan Neja ta Arewa
Rayuwa
Cikakken suna Aliyu Sabi Abdullahi
Haihuwa Jihar Neja, 10 ga Janairu, 1967 (57 shekaru)
ƙasa Nigerian (en) Fassara
Karatu
Makaranta Jami'ar Ahmadu Bello
Harsuna Turanci
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa
Mamba 9th National Assembly of Nigeria (en) Fassara
Imani
Jam'iyar siyasa Peoples Democratic Party
All Progressives Congress

Sana'ar siyasa gyara sashe

Abdullahi ya halarci zaɓen Sanatan Neja ta Arewa a ranar 28 ga Maris, 2015 kuma aka bayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaɓen.[7][8] A watan Fabrairun shekara ta 2019 a zaɓen Sanatan Neja ta Arewa, an sake zaɓensa a matsayin Sanata bayan da ya samu ƙuri’u 161,420, yayin da Honarabul Muhammad Sani Duba na PDP ya samu ƙuri’u 77,109.[9]

Kyauta gyara sashe

A watan Oktoban 2022, shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya ba shi lambar yabo ta ƙasa ta Najeriya kwamandan The Order Of Niger (CON).[10]

Manazarta gyara sashe