Ali Bin Abdul Rahman Al-Huzaify
Ali Bin Abdur Rahman Al Huthaify (an haife shi a ranar 22 ga watan Mayu shekarar 1947) (Larabci; علي بن عبد الرحمن الحذيفي) yana daga cikin Limaman Saudiyya wato Masjid Alharamain kuma mai Khuɗuba a Masallacin Manzon Allah, (S A W) da ke Madina (Khateeb Al-Masjid an-Nabawi) tun a shekarar 1402 A.H har zuwa yanzu, kuma tsohon limamin Masallacin Quba. Yanada salon karatun Alqur'ani ahankali da kuma zurfi.[1]
Ali Bin Abdul Rahman Al-Huzaify | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | Saudi Arebiya, 6 ga Afirilu, 1947 (77 shekaru) |
ƙasa | Saudi Arebiya |
Harshen uwa | Larabci |
Karatu | |
Makaranta | Jami'ar Imam Muhammad ibn Saud Islamic |
Harsuna | Larabci |
Sana'a | |
Sana'a | Liman |
Imani | |
Addini | Musulunci |
Aiki da Karatu
gyara sasheA shekarar 1972 ya kammala karatunsa na digirin farko a fannin shari'a a Jami'ar Musulunci ta Imam Muhammad bin Saud. A shekarar 1975 ya sami digiri na biyu a fannin shari'a a Jami'ar Al-Azhar, sannan ya yi digirinsa ta 3 a jami'ar. Ya kasance limami kuma mai yin khuduba (Khateeb) a Masallacin Quba a shekarar 1978.[2] A shekarar 1979 ya zama limamin Masallacin Manzon Allah (S A W) da ke a Madina (Al-Masjid al-Nabawi). A shekarar 1981 a cikin watan Ramadan an nada shi don ya jagoranci Sallah Tarawihi a Masallacin Harami, bayan karewar watan Ramadan sai ya koma Babban Masallacin Madina inda ya ci gaba da jagorancin Sallah.[3]
Duba Kuma
gyara sasheManazarta
gyara sashe- ↑ "Ali Al huthaify - علي الحذيفي - Holy Quran on Assabile". www.assabile.com. Retrieved October 27, 2019.
- ↑ "أئمة المسجد النبوي - في العهد السعودي ١٣٤٥-١٤٣٦ | عبد الله الغامدي". October 27, 2015. Retrieved October 27, 2019 – via Internet Archive.
- ↑ "Biography - Ali Al Hudhaify - Islamise". www.islamise.co.uk. Retrieved October 27, 2019.