Mohammed Afzal Khan, CBE ( Urdu: محمد افضل خان‎  ; an haife shi a ranar 5 ga watan Afrilu a shekarar 1958) ɗan siyasa ne na Jam'iyyar Labour da ke Burtaniya wanda ke aiki a matsayin Memba na Majalisar (MP) na Manchester Gorton tun 2017 .[1]

Afzal Khan
member of the 59th Parliament of the United Kingdom (en) Fassara

4 ga Yuli, 2024 -
District: Manchester Rusholme (en) Fassara
Election: 2024 United Kingdom general election (en) Fassara
member of the 58th Parliament of the United Kingdom (en) Fassara

12 Disamba 2019 - 30 Mayu 2024
District: Manchester Gorton (en) Fassara
Election: 2019 United Kingdom general election
member of the 57th Parliament of the United Kingdom (en) Fassara

8 ga Yuni, 2017 - 6 Nuwamba, 2019
District: Manchester Gorton (en) Fassara
Election: 2017 United Kingdom general election (en) Fassara
Member of the European Parliament (en) Fassara

1 ga Yuli, 2014 - 8 ga Yuni, 2017 - Wajid Khan, Baron Khan of Burnley
District: North West England (en) Fassara
Election: 2014 European Parliament election (en) Fassara
107. Lord Mayor of Manchester (en) Fassara

2005 - 17 Mayu 2006
Tom O'Callaghan (en) Fassara - James Ashley (en) Fassara
Shadow Deputy Leader of the House of Commons (en) Fassara

Rayuwa
Haihuwa Jhelum (en) Fassara, 5 ga Afirilu, 1958 (66 shekaru)
ƙasa Birtaniya
Harshen uwa Turanci
Karatu
Harsuna Turanci
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa da solicitor (en) Fassara
Wurin aiki Strasbourg da City of Brussels (en) Fassara
Kyaututtuka
Imani
Jam'iyar siyasa Labour Party (en) Fassara
afzalkhan.org.uk

Ya kasance tsohon magajin garin Manchester tsakanin shekarun ta 2005-2006, kuma ya yi aiki a matsayin memba na Majalisar Tarayyar Turai (MEP) na Arewacin Yammacin Ingila daga 2014 zuwa 2017.[2]

An haifi Khan a ƙasar Pakistan kuma ya zo Birtaniya yana da shekaru 11. Bayanu ya bar makaranta ba tare da takardar shaida kammala karatu ba, yana da ayyuka da yawa, ciki har da matsayin ɗan sanda na Greater Manchester, kafin ya koma karatu ya kuma cancanci zama lauya.[3]

Harkar siyasa

gyara sashe

Karamar hukuma

gyara sashe

An fara zabar Khan a matsayin Kansilan Labour a 2000, an sake zaɓan shi a 2004, 2007 da 2011, don wakiltar Cheetham Ward. Ya yi aiki a matsayin Babban Memba na Harkokin ƙananan Yara.

Khan ya zama Musulmi na farko da ya riƙe matsayin Magajin Garin Manchester, inda ya dauki matsayi na 2005-2006.

A shekarar 2010, an nada Khan CBE don aikin kan dangantakar launin fata.

A shekarar 2011 ne, aka ba da shawarar Khan a matsayin ɗan takarar Oldham East da Saddleworth . A cikin 2012, ya kasance dan takara mai yuwuwa don zaben Bradford West amma ya rasa zabin Imran Hussain, wanda dan takarar jam'iyyar Respect, George Galloway ya kayar da shi.

Majalisar Turai

gyara sashe

An zaɓi Khan a watan Fabarairu 2013 a cikin jerin Jam'iyyar Labour na Arewacin Yammacin Ingila a zaɓen 'yan majalisar Turai na 2014 kuma, a ranar 22 ga Mayu 2014, an mayar da shi a matsayin MEP ga Majalisar Turai don wakiltar Arewacin Yammacin Ingila .

A watan Janairun 2016, Jam'iyyar Progressive Alliance of Socialists and Democrats na Majalisar Tarayyar Turai ta nada Khan a matsayin wakili na musamman ga al'ummomin Musulmi. A cikin wannan aiki, Khan ya ziyarci Jamus, Birtaniya, Italiya, Faransa da Denmark don yin aiki tare da al'ummomin musulmi na gida tare da gayyatar kungiyoyin matasa musulmai zuwa majalisar.

 
Khan yana yakin neman zabe tare da shugaban jam'iyyar Labour Jeremy Corbyn a wani bangare na zaben Manchester Gorton da aka soke.

Aikin majalisa

gyara sashe

A watan Maris 2017, ya nemi zama dan takarar Labour a zaɓen fidda gwani na Manchester Gorton na 2017 kuma an zaɓe shi bisa hukuma a ranar 22 ga Maris. A yayin zaɓen fidda gwanin ya ce "Na yi Allah-wadai da kalaman da Ken Livingstone ya yi kuma na yi imanin cewa babu wurin kyamar Yahudawa a jam'iyyar Labour." Ya kara da cewa, “Na kasance mai fafutukar yaki da wariyar launin fata da kyamar Yahudawa. A watan 2008, an ba ni lambar yabo ta CBE a wani bangare na aikin da na karfafa fahimtar juna tsakanin Musulmi da Yahudawa. Ina da niyyar ci gaba da wannan aikin idan aka zabe ni a matsayin ɗan majalisar wakilai na Manchester Gorton."

 
Afzal Khan

An soke zaben bayan rusa majalisar dokokin da aka yi a farkon babban zaben ranar 8 ga watan Yunin 2017 . An sake zabar Khan a matsayin dan takarar jam'iyyar Labour a babban zaben kasar kuma an zabe shi, ya zama dan majalisar musulmi na farko a Manchester. A cikin Yuli 2017, Khan an nada shi Ministan Shige da Fice.

A watan Yulin 2019, Khan ya nemi afuwa saboda bidiyo da wani dan wasa ya yada a Facebook shekaru biyu da suka gabata Benjamin Netanyahu. Rubutun da ke ƙarƙashin faifan bidiyon yana magana ne akan "Isra'ila-British-Swiss-Rothschilds laifuffuka" da "jama'a kisan gillar Rothschilds Isra'ila maƙaryata masu laifi". Khan ya ce ya “ji dadi”, ya kara da cewa “Ban karanta rubutun da ke kasa ba, wanda ke dauke da wata makarkashiyar kyamar Yahudawa game da Rothschilds. Ba zan taba raba shi ba idan na ga haka."

Sauran ayyuka

gyara sashe

Tsakanin 2000 zuwa 2004, Khan ya kasance memba na Sashen Ciniki da Masana'antu na Ma'aikatar Kasuwancin tsirarun Kabilanci, yana ba da shawara ga Sakatariyar Harkokin Waje, Patricia Hewitt .

Bayan harin bam da aka kai a Landan a shekara ta 2005, ya zama memba na ƙungiyar aiki na Ofishin Cikin Gida da nufin hana tsattsauran ra'ayi.

Ya kuma taɓa zama Mataimakin Sakatare-Janar na Majalisar Musulmi ta Biritaniya kuma shi ne wakilinta na Arewa maso Yamma.

Shi ne wanda ya kafa kungiyar Musulmai da Yahudawa ta Babban birnin Manchester.

Khan ya sha fitowaa shirye-shiryen Channel M.

 
Afzal Khan

An nada shi a matsayin shugaban majalissar ma'aikata musulmai watoLabour Muslim Network a watan Agusta 2020. [4]

Sauran abubuwan da suka faru

gyara sashe
 
Afzal Khan tare da wasu jaruman india

A watan Maris 2018, Khan ya sami wani fakitin tuhuma wanda ke ɗauke da wasiƙar adawa da Musulunci da ruwa mai ɗaci. Daga baya an gano sinadarin ba shi da illa. An samu irin wannan fakitin takwarorinsu na jam'iyyar Labour, Mohammad Yasin, Rushanara Ali da Rupa Huq .

'Yar Khan Maryam ta kasance Kansila na Majalisar Birnin Manchester, na Longsight .

Duba kuma

gyara sashe
  • Jerin 'yan Pakistan na Burtaniya
  • Abokan Kwadago na Falasdinu & Gabas ta Tsakiya

Manazarta

gyara sashe
  1. "Manchester Rusholme - General election results 2024". BBC News.
  2. http://www.uaeinteract.com/docs/Sultan_meets_Mayor_of_Manchester/19319.htm
  3. "The Executive Members in 2019 / 2020 | The Members of the Executive | Manchester City Council"
  4. Afzal appointed Parliamentary Chair of Labour Muslim Network. Afzal Khan (2020-08-05). Retrieved 2020-11-27.