Adewale Oluwatayo (1950–2016) [1] ɗan majalisar wakilai ne mai wakiltar mazaɓar Ifako-Ijaye ta tarayya ta Legas. Ya yi shugaban ƙaramar hukumar Ifako-Ijaiye a tsakanin shekarun 2004 zuwa 2007. Ya yi aiki a matsayin mai ba da shawara na musamman kan ilimi ga gwamnatin jihar Legas daga shekarun 2009 zuwa 2011. [2] [3] [4]

Adewale Oluwatayo
mamba a majalisar wakilai ta Najeriya,

Rayuwa
ƙasa Najeriya
Harshen uwa Yarbanci
Karatu
Harsuna Turanci
Yarbanci
Pidgin na Najeriya
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa

Rayuwar farko da ilimi

gyara sashe

Adewale ya halarci makarantar nahawu ta Ilesha kuma a shekarar 1968, ya samu takardar shedar makarantar sa ta yammacin Afirka. Ya yi digirinsa na farko a Jami’ar Najeriya da ke Nsukka a shekarar 1979. A shekarar 2005, ya sami takardar shaidar digiri na biyu a Jami'ar Jihar Legas. [1] [2]

Daga shekarun 2004 zuwa 2007, Adewale ya zama shugaban ƙaramar hukumar Ifako/Ijaiye. A tsakanin shekarar 2009 zuwa 2011, an naɗa shi a matsayin mai bawa gwamnatin jihar Legas shawara ta musamman kan harkokin ilimi a zamanin Gwamna Babatunde Fashola. [5] [6]

A shekarar 2015 ya lashe zaɓen majalisar wakilai ta tarayya a ƙarƙashin jam’iyyar APC (All Progressive Congress) don wakiltar mazaɓar Ifako-Ijaiye na tarayya. [1]

Manazarta

gyara sashe
  1. 1.0 1.1 1.2 vanguard (2016-07-21). "Lagos Rep, Adewale Oluwatayo is dead". Vanguard News (in Turanci). Retrieved 2024-12-10. Cite error: Invalid <ref> tag; name ":1" defined multiple times with different content
  2. 2.0 2.1 "House of Reps member dies". www.premiumtimesng.com. Retrieved 2024-12-10. Cite error: Invalid <ref> tag; name ":0" defined multiple times with different content
  3. BellaNaija.com (2016-07-21). "House of Reps Member Adewale Oluwatayo Passes On". BellaNaija (in Turanci). Retrieved 2024-12-10.
  4. Shibayan, Dyepkazah (2016-07-21). "House of reps member found dead". TheCable (in Turanci). Retrieved 2024-12-10.
  5. Oluwagbemi, Ayodele (2016-07-21). "Lagos Rep, Adewale, dies". Punch Newspapers (in Turanci). Retrieved 2024-12-10.
  6. Sesan (2016-07-22). "Lagos Rep Elijah dies, Dogara, others mourn". Punch Newspapers (in Turanci). Retrieved 2024-12-10.