Adamu Talba Gwargwar
Adamu Garba Talba (an haife shi a ranar 15 ga watan Agustan shekarar alif dari tara da hamsin da biyu 1952) tsohon sanata ne kuma dan siyasa a Najeriya da ya fito daga shiyyar arewa maso gabas. Dan asalin kabilar Karaikarai da ake kira Birkayi ne kuma mahaifar sa ita ce garin Tikau dake karamar hukumar Nangere a Jihar Yobe. Yana daya daga 'ya'yan marigayi tsohon Sarkin Tikau mai martaba Alhaji Abubakar Talba Shuwa sannan yana daya daga jerin masu sarautar gargajiya na fadar masarautar Tikau.[1] Ya zama zaeabben Sanata mai wakiltar shiyyar Yobe ta Kudu ne a ranar 29 ga watan Mayun shekarar 2007 a karkashin inuwar jam'iyyar PDP.
Adamu Talba Gwargwar | |||
---|---|---|---|
5 ga Yuni, 2007 - 6 ga Yuni, 2011 District: Yobe South | |||
Rayuwa | |||
Haihuwa | Jihar Yobe, 15 ga Augusta, 1952 (72 shekaru) | ||
ƙasa | Najeriya | ||
Harshen uwa | Hausa | ||
Karatu | |||
Makaranta | Jami'ar Kimiyya da Fasaha ta Kano | ||
Harsuna |
Turanci Hausa Pidgin na Najeriya | ||
Sana'a | |||
Sana'a | ɗan siyasa | ||
Imani | |||
Jam'iyar siyasa | Peoples Democratic Party |
Karatu
gyara sasheTalba yayi karatun difloma a bangaren iya kula da gudanuwar mulki. Daganan sai ya shiga aikin gwamnati a jihar Yobe. Ya taba zama shugaban karamar hukumar Nangere sau biyu a jihar Yobe. An nada shi Shugaban Hukumar Gudanarwa, Cibiyar Kiwon Lafiya ta Tarayya, Alare, kuma ya taba rike mukamin Darakta na NNDC, Kaduna har wa yau kuma ya taba kasancewa Kwamishinan Lafiya na Jihar Yobe.[2]
Ayyuka da Nasarori
gyara sasheA matsayinsa na Sanata, a watan Satumban shekarata 2008, Talba ya ba da shawarar kafa Kwamitin Hamada na Kasa don magance matsalar kwararar Hamada a yankin arewacin kasar.