Ibrahim Adamu Gumba (an haife shi a ranar 10 ga watan Oktoban shekarar alif dari tara da arba'in da takwas 1948) ɗan siyasan Najeriya ne , kuma an zaɓe shi Sanata a mazabar Bauchi ta Kudu na jihar Bauchi, Najeriya a zaɓen ƙasa na watan Afrilu na shekara ta 2011 da ya gabata. Ya yi takarar tikitin jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP).[1]

Adamu Gumba
mamba a majalisar dattijai ta Najeriya

6 ga Yuni, 2011 - 6 ga Yuni, 2015
District: Bauchi South
Rayuwa
Haihuwa 10 Oktoba 1948 (76 shekaru)
ƙasa Najeriya
Harshen uwa Hausa
Karatu
Harsuna Turanci
Hausa
Pidgin na Najeriya
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa
Imani
Jam'iyar siyasa Peoples Democratic Party

Farkon rayuwa

gyara sashe

An haifi Gumba a ranar 10 ga watan Oktoba shekarar 1948. Ya samu BSc a Gwamnati. Ya yi aiki a Hukumar Kwastam ta Najeriya, inda ya kai matsayin Mataimakin Kwanturola Janar.[2] Gumba ya zama Shugaban Ma'aikatan Gwamnatin Jihar Bauchi.[3] A shekara ta 2006, an naɗa shi Kwamishinan Ilimi a jihar Bauchi.[4]

Kujerar sanatan Bauchi ta Kudu ta zama babu kowa a cikin watan Mayun shekarar 2010 bayan da Shugaba Goodluck Jonathan ya nada Sanata Bala Muhammed Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT).[5] A zaɓen 23 ga watan Agusta na shekarar 2010 na kujerar sanatan Bauchi ta Kudu, Gumba ya samu kuri'u 273,764, yayin da Ibrahim Haruna na jam'iyyar All Nigeria People's Party (ANPP) ke biye masa da kuri'u 57,661, Danjuma Dabo na jam'iyyar Congress for Progressive Change (CPC) ya samu 56,294 kuri'u.[6]

A zaɓen fidda gwani na jam'iyyar PDP na zaɓen kujerar sanatan Bauchi ta Kudu a watan Afrilun 2011, Gumba ya samu takarar ne a karkashin tsohon sanata Abubakar Maikafi da kwamishinan zabe na kasa mai zaman kanta (INEC) na kasa, Mohammed Abubakar.[7] A zaben, Gumba ya samu kuri'u 312,627, yayin da Alhaji Mohammed Ibrahim na jam'iyyar All Nigeria People's Party (ANPP) ya samu kuri'u 114,281.[8] Sanata Malam Wakili ya gaji Sanata Gumba a majalisar dattijai bayan ya doke Isa Yuguda a babban zaɓen watan Maris na 2015.

Manazarta

gyara sashe
  1. "2019: Gumba joins Bauchi PDP governorship ticket race - Daily Trust". dailytrust.com. Retrieved 2023-06-02.
  2. https://nass.gov.ng/nass/portfolio/profile.php?id=Sen.adamu.gumba.ibrahim Archived 2021-10-21 at the Wayback Machine
  3. https://web.archive.org/web/20160303193036/http://www.triumphnewspapers.org/wa2072010.html
  4. https://web.archive.org/web/20121007194347/http://www.afdevinfo.com/htmlreports/peo/peo_3393.html
  5. https://web.archive.org/web/20110823021413/http://ndn.nigeriadailynews.com/templates/?a=29618
  6. http://news2.onlinenigeria.com/news/breaking-news/56567-PDP-candidate-wins-Bauchi-senatorial--election.rss
  7. "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2016-03-03. Retrieved 2023-03-23.
  8. http://www.elombah.com/news/node/5006?page=8[permanent dead link]