Acyl Ahmat
Ahmat Acyl (an haifeshi a shekara ta 1944 ya Mutu a 1982) ya kasance Balaraben Chadi [1] kuma shugaban tawaye ne a lokacin Yaƙin basasar ƙasar Chadi.
Acyl Ahmat | |||||
---|---|---|---|---|---|
1979 - ga Yuni, 1982 - Idriss Miskine →
| |||||
Rayuwa | |||||
Haihuwa | Faransa Equatorial Afirka, 1944 | ||||
ƙasa | Cadi | ||||
Mutuwa | 1982 | ||||
Karatu | |||||
Harsuna |
Larabci Faransanci | ||||
Sana'a | |||||
Sana'a | Mai wanzar da zaman lafiya da ɗan siyasa |
Tarihin Rayuwa
gyara sasheA karkashin mulkin Tombalbaye, Acyl ya kasance mataimaki a Majalisar Kasar na Batha . [2] A shekarar 1976 ya koma cikin 'yan tawaye, ta hanyar shiga wata karamar rundunar sojin larabawan dake kasar Libya. Tare da goyon bayan Muammar Gaddafi, Shugaban Libya, ya taba nuna adawa ga shugaban rundunar Mohamed Baghlani, kuma lokacin da shi din ya mutu a hatsarin mota a Tripoli a shekarar 1977, ba tare da bata lokaci ba aka naɗa Acyl sabon shugaban rundunar mayakan. Daga wannan lokacin kuma, aka san shi a matsayin mutumin Gaddafi a Chadi. [3]