Abu-Abdullah Adelabu
Abdul-Fattah Abu-Abdullah Taiye Ejire Adelabu (da larabci|عبد الفتّاح أبو عبد الله تَائيي أيجيري أديلابو) ko Sheikh Adelabu, kuma ana kiransa da Al-Afriqi (larabci|الإفريقي) ko Shaykh Al-Afriqi (larabci|الشيخ الإفريقي) yakasance Dan Nijeriya ne, malamin addinin musulunci, Marubuci, malamin jami'a, mawallafi kuma mai wa'azi dan asalin birnin Osogbo babban birnin Jihar Osun, Nijeriya.
Abu-Abdullah Adelabu | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | Osogbo, |
ƙasa | Najeriya |
Ƙabila | Yaren Yarbawa |
Harshen uwa | Yarbanci |
Karatu | |
Harsuna |
Turanci Yarbanci Larabci Pidgin na Najeriya |
Sana'a | |
Sana'a | Malami |
Imani | |
Addini | Musulunci |
Adelabu ya karanta ilimin addinin musulunci a garin Damascus, dake kasar Syria, wanda yasamu nasarar yin Postgraduate Diploma, digiri na biyu (masters), da ta uku (Ph.D).