Abiodun Olujimi
Abiodun Christine Olujimi (an haife ta a ranar 25ga watan Disamba 1958) 'yar siyasa ce a Najeriya.[1] Abiodun 'yar majalisar dattijai ce ta Tarayyar Najeriya mai wakiltar mazabar Ekiti ta Kudu[2] kuma shugaban marasa rinjaye na majalisar dattijan Najeriya.[3] Ta kasance mamba a hukumar sadarwa ta Najeriya.[1]
Abiodun Olujimi | |||||
---|---|---|---|---|---|
11 ga Yuni, 2019 - 11 ga Yuni, 2023 - Yemi Adaramodu → District: Ekiti South
9 ga Yuni, 2015 - 9 ga Yuni, 2019 ← Abiodun Olujimi District: Ekiti South | |||||
Rayuwa | |||||
Cikakken suna | Abiodun Christine Olujimi | ||||
Haihuwa | Omuo (en) , 25 Disamba 1958 (65 shekaru) | ||||
ƙasa | Najeriya | ||||
Karatu | |||||
Makaranta | Jami'ar Abuja | ||||
Matakin karatu |
diploma (en) Digiri a kimiyya postgraduate degree (en) | ||||
Harsuna |
Turanci Pidgin na Najeriya | ||||
Sana'a | |||||
Sana'a | ɗan siyasa | ||||
Imani | |||||
Jam'iyar siyasa | Peoples Democratic Party |
Rayuwar farko da ilimi
gyara sasheAn haife ta a Omuo Ekiti, jihar Ekiti, ta fara karatu ne a makarantar Our Lady of Apostles da ke garin Ibadan, jihar Oyo sannan ta zarce zuwa makarantar koyan ayyukan Jarida ta Najeriya wato Nigerian Institute of Journalism don samun difloma a shekara ta 1976. Biodun Olujimi ta kuma samu digiri a fannin kimiyyar siyasa da kuma digiri na biyu a fannin hulda da jama'a da kasuwanci daga jami'ar Abuja.[4]
Ayyuka
gyara sasheBiodun ta fara aikin ta ne a matsayin mai watsa labarai kuma 'yar jarida.[5] A lokacin da take aikin labarai, tayi aiki da jaridar Nigerian Tribune, Nigerian Post and Telecommunication, Nigerian Television Authority, Delta Steel Company, Ovwian Aladja, Reflex Concept, DBN Television kuma ta kasance Manajan DBN TV daga 1993 zuwa 1997.[6]
Siyasa
gyara sasheTa shiga siyasa tare da mijinta a 1997 a matsayin Sakatariyar Yada Labarai ta Jam’iyyar NCPN da ta mutu, ta koma All Peoples Congress (APC) bayan mutuwar tsohuwar jam’iyyarta, kuma har wayau ta zama Sakatariyar Yada Labarai ta Kasa a APC.
A cikin shekara ta 2002 ne, ta koma jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) kuma wannan shine farkon samun nasarar ta a fagen siyasa. A shekara ta 2003 aka zabe ta matsayin mataimakiyar Gwamnan Jihar Ekiti, daga nan kuma aka zabe ta ta zama 'yar Majalisar Dokoki ta Tarayya. Ta zama Mataimakiyar Gwamnan Jihar Ekiti tare da Gwamna Ayo Fayose a shekara ta 2005. Olujimi ya sami wasu manyan matsayi a siyasa; daga matsayin kwamishina mai kula da ayyuka da kayan more rayuwa a jihar ta har zuwa Daraktar harkokin mata. A shekara ta 2015, ta yi takarar kujerar Sanata kuma ta yi nasara, sannan ta zama sanata mai wakiltar mazabar Ekiti ta Kudu a Majalisar Tarayya a karkashin Jam’iyyar PDP.[4]
Ana daukar Abiodun Olujimi a matsayin daya daga cikin gogaggun mata ‘yan siyasa a Najeriya.
Jam’iyyar Peoples Democratic Party, reshen jihar Ekiti ta nada ta a matsayin shugabar jam’iyyar ta jihar a watan Nuwamban shekara ta 2018 domin karfafa jam’iyyar a jihar don shirye-shiryen zaben 2019. Ojomoyela, Rotimi. "Mun tsaya tare da Olujimi a matsayin jagoranmu a Ekiti, in ji kungiyar PDP". Vanguard Media Limited, Najeriya. Vanguard, Nigeria. An dauka a 11 Maris 2019.[7]
A zaben shekara ta 2019, da farko ta rasa kujerarta na matsayin wakiliyar Ekiti ta Kudu ga dan takarar APC Prince Adedayo Clement Adeyeye.[8][9] Koyaya, Kotun Zabe ta Majalisar Jiha da Kotun daukaka kara daga baya sun ayyana ta matsayin wacce ta lashe zaben Sanatan na Kudancin Ekiti. Sakamakon haka, Shugaban Majalisar Dattawan ya rantsar da ita a Majalisar Dattawan Najeriya a ranar 14 ga Nuwamba, 2019.[10]
A ranar 22 ga watan March 2021 ne, sanata Abiodun Olujimi ta bada labarin yadda ta tsira daga harbin bindiga a yayin da ake sake zaben kujerar majalisar dokoki na mazabar Ekiti ta kudu. An sake zaben ne don maye gurbin marigayi Juwa Adegbuyi, wanda ya mutu[11] a kan kujerar a cikin watan Febreru.[12]
Manazarta
gyara sashe- ↑ 1.0 1.1 "IT & Telecom, Digest (2 March 2017). "Senator Abiodun Olujimi Is Diligent". IT & Telecom Digest. Retrieved 8 March 2018.
- ↑ "Ekiti PDP Primary: Senator Olujimi steps down - The Nation Newspaper". thenationonlineng.net. Retrieved 18 March 2022.
- ↑ "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2019-11-17. Retrieved 2020-11-22.
- ↑ 4.0 4.1 Defenders, Ekiti. "Read Full Biography And Life History Of Abiodun Olujimi". No. 7 February 2018. Archived from the original on 10 March 2018. Retrieved 9 March 2018.
- ↑ Baiyewu, Leke. "I wanted to be a doctor but somehow couldn't – Senator Olujimi". No. 11 March 2017. Punch. Retrieved 9 March 2018.
- ↑ National Assembly, Federal Republic of Nigeria. "Sen. BIODUN CHRISTINE OLUJIMI Ekiti South". National Assembly. Archived from the original on 10 March 2018. Retrieved 8 March 2018.
- ↑ "Ojomoyela, Rotimi (8 November 2017). "We stand with Olujimi as our leader in Ekiti, says PDP group". Vanguard Media Limited, Nigeria. Retrieved 11 March2019.
- ↑ "End of the Road for Dayo Adeyeye?". THISDAYLIVE. 26 January 2020. Retrieved 18 May2021.
- ↑ "PDP senators Olujimi, Faseyi lose reelection bid in Ekiti". Punch Newspapers. Retrieved 28 February2019.
- ↑ "Fayose, Olujimi in verbal war over Ekiti PDP ward congress". Vanguard News. 9 March 2020. Retrieved 18 May 2021.
- ↑ "Ekiti House Of Assembly Member, Juwa Adegbuyi Is Dead". Channels Television. Retrieved 6 April2022.
- ↑ "How I escaped gunshots during Ekiti bye-election – Senator". 22 March 2021. Retrieved 15 May2021.