Yemi Adaramodu
Yemi Adaramodu ɗan siyasar Najeriya ne kuma zababben Sanata mai wakiltar mazabar Ekiti ta Kudu a majalisar dattawa ta 10 a kan tikitin jam'iyyar All Progressives Congress, APC. Ya kasance shugaban ma’aikata na gwamnan jihar Ekiti sannan aka zabe shi a matsayin dan majalisar wakilai ta tarayya
Yemi Adaramodu | |||
---|---|---|---|
11 ga Yuni, 2019 - | |||
Rayuwa | |||
Haihuwa | 17 Nuwamba, 1986 (38 shekaru) | ||
ƙasa | Najeriya | ||
Karatu | |||
Harsuna |
Turanci Pidgin na Najeriya | ||
Sana'a | |||
Sana'a | ɗan siyasa | ||
Mamba | Majalisar Wakilai (Najeriya) | ||
Imani | |||
Jam'iyar siyasa | All Progressives Congress |
Wannan mukalar bata da Reference (Manazarta) ko daya, ka taimaka ta hanyar samar da Manazarta daga littafi ko yanar gizo, duba wannan shafin domin samun masaniya akan yanda zaka samar da Reference (Manazarta) a cikin wannan mukalar.
. |
Siyasa
gyara sasheAdaramodu ya fara harkar siyasa ne biyo bayan nadinsa a matsayin shugaban ma’aikatan gwamnan jihar Ekiti. Bayan haka ne aka zabe shi a matsayin dan majalisar wakilai ta tarayya sannan ya zama shugaban kwamitin ci gaban matasa. Ya tsaya takara a zaben Sanata mai wakiltar Ekiti ta Kudu a ranar 25 ga Fabrairu, 2023 da Sanata mai ci kuma tsohon shugaban marasa rinjaye na majalisar dattawa, Abiodum Olujimi na jam’iyyar People’s Democratic Party, PDP.[2] Adaramodu ya samu kuri’u 63,189 inda ya doke Olujimi wanda ya samu kuri’u 36,191. Nasarar Adaramodu a zaben ya samu sauki sakamakon rikicin jam’iyyar abokin hamayyarsa wanda ya sanya wasu magoya bayan abokin hamayyarsa suka yi masa aiki a zaben.