Farfesa Abdul Ganiyu Ambali (an haife shi ranar 29 ga watan Nuwamba, shekarar 1957) malami ne ɗan Najeriya, shugaba kuma tsohon mataimakin shugaban jami'ar Ilorin. Ambali ya kuma kasance tsohon shugaban kungiyar jami'o'in Afirka ta Yamma (AWAU), kuma wanda ya samu babbar lambar yabo ta Najeriya, CON.[1][2][3][4][5]

Abdul Ganiyu Ambali
Rayuwa
Haihuwa Ilorin, 29 Nuwamba, 1957 (66 shekaru)
ƙasa Najeriya
Karatu
Makaranta University of Liverpool (en) Fassara
Jami'ar Ahmadu Bello
Harsuna Turanci
Yarbanci
Pidgin na Najeriya
Sana'a
Sana'a Malami da researcher (en) Fassara
Employers Jami'ar Maiduguri
Jami'ar Ilorin
Imani
Addini Musulunci

Farkon rayuwa gyara sashe

An haifi Abdul Ganiyu Ambali a garin Ilorin, Jihar Kwara ga dangin Mall. Ambali Gidado da Mrs. Hussaina Angulu. Ambali ya kuma yi karatun firamare a makarantar firamare ta Pakata, Ilorin, bayan gama firamare ya wuce makarantar sakandare ta McBride a Jalingo, (yanzu makarantar sakandaren gwamnati, Jalingo) a jihar Taraba. Abdul ya samu gurbin karatu daga gwamnatin jihar Borno don yin digiri na farko a fannin likitancin dabbobi a jami’ar Ahmadu Bello ya kammala karatun jami'a a shekarar 1981. Ya yi digirinsa na biyu (Masters) da Digiri na biyu a Jami'ar Liverpool ta Burtaniya. Ambali ya zama Memba na Kwalejin Likitocin Dabbobi na Najeriya, (MCVSN) a shekarar 2004 da na kwalejin Veterinary na Surgeons of Nigeria (FCVSN) a 2009.

Manazarta gyara sashe

  1. "The Vice-Chancellor". www.unilorin.edu.ng (in Turanci). Archived from the original on 9 May 2017. Retrieved 14 May 2017.
  2. "Tribute to Prof. AbdulGaniyu Ambali, an uncommon leader @ 59. By Kunle Akogun | #Ilorin, #Kwara News | @IlorinInfo". www.ilorin.info. Retrieved 14 May 2017.
  3. "LinkedIn". Retrieved 12 August 2017.
  4. "Abdulganiyu Ambali – Google Scholar Citations". scholar.google.com. Retrieved 12 August 2017.
  5. "Prof. Abdulganiyu Ambali pagesepsitename%%". Channels Television. Retrieved 12 August 2017.