Abdul-Aziz Ayaba Musah
Abdul-Aziz Ayaba Musah ɗan siyasar Ghana ne kuma ɗan majalisa mai wakiltar mazabar Mion.[1] An zaɓe shi a lokacin dan majalisa na shekarar 2020, inda ya zama dan majalisa na farko da ya yi nasara akan tikitin New Patriotic Party a mazabar Mion.[2]
Abdul-Aziz Ayaba Musah | |||
---|---|---|---|
7 ga Janairu, 2021 - District: Mion Constituency (en) | |||
Rayuwa | |||
Haihuwa | Sang, 1 ga Janairu, 1986 (38 shekaru) | ||
ƙasa | Ghana | ||
Karatu | |||
Makaranta | Jami'ar Nazarin Ci Gaban | ||
Harsuna | Turanci | ||
Sana'a | |||
Sana'a | ɗan siyasa | ||
Imani | |||
Addini | Musulunci | ||
Jam'iyar siyasa | New Patriotic Party |
Rayuwar farko da ilimi
gyara sasheAn haife shi a ranar 1 ga watan Janairun shekarar 1986, kuma ya fito ne daga garin Sang a yankin Arewacin Ghana. Ya yi SSSCE a shekarar 2005. A shekarar 2017 ya samu takardar shaidar kammala digiri a fannin aikin gwamnati sannan a shekarar 2010 ya kara samun digiri a fannin tattalin arziki.[3]
Aiki
gyara sasheYa kasance ma’aikacin bautar kasa a Hukumar Inshorar Lafiya ta Kasa, sannan kuma mai kula da ma’aikatan kananan hukumomi. Shi ne Babban Manaja na Kamfanin Alhaji Musah.[3]
Aikin siyasa
gyara sasheDan jam'iyyar NPP ne kuma a halin yanzu dan majalisa mai wakiltar mazabar Mion. Ya lashe zaben ne da kuri'u 21,552 yayin da Mohammed Abdul Aziz na jam'iyyar NDC ya samu kuri'u 14,158. Kwace kujerar da Abdul Aziz ya yi ya kafa tarihi domin shi ne karon farko da jam'iyyar NPP ta lashe mazabar Mion cikin shekaru 28.[4][5][6]
A shekarar 2021, an rantsar da Abdul-Aziz tare da Alexander Kwamena Afenyo-Markin, Johnson Kwaku Adu, Laadi Ayii Ayamba da Emmanuel Kwasi Bedzrah a lokacin babban zama na shekarar 2021, na Majalisar ECOWAS wanda ya faru a Freetown na kasar Saliyo.[7]
Kwamitoci
gyara sasheShi mamba ne na Kwamitin Kasafin Kudi na Musamman sannan kuma memba ne a Kwamitin Samar da Ayyuka, Jin Dadin Jama'a da Kamfanonin Jiha.[3]
Rayuwa ta sirri
gyara sasheAbdul Aziz musulmi ne.[3]
Tallafawa
gyara sasheA shekarar 2020, ya ba da kyautar babur ga Sarkin Jagrido a yankin Arewacin Ghana.[8]
Manazarta
gyara sashe- ↑ "Parliament of Ghana". www.parliament.gh. Retrieved 26 December 2021.
- ↑ FM, Peace. "Mion Constituency Results - Election 2020". Ghana Elections - Peace FM. Retrieved 26 December 2021.
- ↑ 3.0 3.1 3.2 3.3 "Parliament of Ghana". www.parliament.gh. Retrieved 2022-01-16.
- ↑ "NPP Breaks Record In Mion". DailyGuide Network (in Turanci). 2020-12-15. Retrieved 2022-01-16.
- ↑ "NPP wins Mion seat for the first time". GhanaWeb (in Turanci). 2020-12-12. Retrieved 2022-01-16.
- ↑ "Musah Abdul Aziz Ayaba Archives — Kasapa102.5FM" (in Turanci). Archived from the original on 2022-01-16. Retrieved 2022-01-16.
- ↑ author; ANAETO, Fred (2021-03-29). "1st Extraordinary Session 2021 of ECOWAS Parliament: Adoption of the Strategic Plan (2020-2024) as the first priority". ECOWAS Parliament Website (in Turanci). Retrieved 2022-02-04.
- ↑ Admin. "NPP Mion Parliamentary Candidate donates to Konkomba Chief | The Custodian Online" (in Turanci). Retrieved 2022-01-16.