Johnson Kwaku Adu
Johnson Kwaku Adu (an haife shi a ranar goma 10 ga watan Agusta shekara ta, alif dubu daya da dari tara da sittin da tara 1969) ɗan siyasan Ghana ne kuma memba na majalisar dokoki ta bakwai na Jamhuriyyar Ghana ta huɗu kuma majalissar ta takwas 8 ta Jamhuriyyar Ghana ta huɗu, mai wakiltar mazabar Ahafo Ano ta Kudu maso yamma a yankin Ashanti akan tikitin. na New Patriotic Party.[1][2]
Johnson Kwaku Adu | |||||||
---|---|---|---|---|---|---|---|
7 ga Janairu, 2021 - District: Ahafo Ano South West Constituency (en) Election: 2020 Ghanaian general election (en)
7 ga Janairu, 2017 - District: Ahafo Ano South West Constituency (en) Election: 2016 Ghanaian general election (en)
7 ga Janairu, 2013 - 6 ga Janairu, 2016 District: Ahafo Ano South West Constituency (en) Election: 2012 Ghanaian general election (en) | |||||||
Rayuwa | |||||||
Haihuwa | Yankin Ashanti, 10 ga Augusta, 1969 (55 shekaru) | ||||||
ƙasa | Ghana | ||||||
Harshen uwa | Twi (en) | ||||||
Karatu | |||||||
Makaranta |
Jami'ar Ilimi, Winneba diploma (en) Jami'ar Ilimi, Winneba Bachelor of Education (en) : ilmi | ||||||
Harsuna |
Turanci Twi (en) | ||||||
Sana'a | |||||||
Sana'a | ɗan siyasa da Malami | ||||||
Imani | |||||||
Addini | Kiristanci | ||||||
Jam'iyar siyasa | New Patriotic Party |
Rayuwar farko da ilimi
gyara sasheAn haifi Adu a ranar goma 10 ga watan agusta a shekara ta, alif dubu daya da dari tara da sittin da tara 1969 a Akrokerri a cikin yankin Ashanti. Ya sami Diploma a Chemistry/ a shekara ta, dubu biyu 2000. Ya sami BEd (Science) a Jami'ar Ilimi, Winneba a shekarar, dubu biyu da daya 2001.[1]
Rayuwa ta sirri
gyara sasheAdu Kirista ne kuma abokin tarayya a Cocin Fentikos.[1] Yana da aure da ’ya’ya biyu.[3]
Aiki
gyara sasheAdu ya kasance kodinetan NADMO na gundumar Ahafo Ano ta kudu daga shekarar dubu biyu da biyu 2002 zuwa shekarar alif dubu biyu da tara 2009, da kuma ofishin kula da harkokin ilimi na Ghana (Circuit Supervisor) Ahafo Ano District Office daga shekarar, dubu biyu da goma 2010 zuwa shekarar alif dubu biyu da goma sha biyu 2012.[3] Sannan ya kasance malami mai koyar da kimiyya a Kwalejin Ilimi ta Akrokeri.[3]
Rayuwar siyasa
gyara sasheAdu dan jam'iyyar NPP ne.[4][5][6] Ya kasance dan majalisa mai rinjaye a majalisar dokoki ta 6 a jamhuriya ta hudu 4 ta Ghana. Ya kasance Shugaban Majalisar Wakilan Ahafo Ano ta Kudu, Mankraso, daga watan Afrilu shekara ta , dubu biyu da tara 2009 zuwa Janairu shekarar alif dubu biyu da goma sha ukku 2011; da MP daga watan Janairu shekara ta, dubu biyu da goma sha ukku 2013 zuwa yau; zangonsa na biyu kenan.[3]
Ya tsaya takara a babban zaben Ghana na shekarar, dubu biyu da ashirin 2020 akan tikitin New Patriotic Party kuma ya lashe zaben wakilci a majalisar wakilai ta takwas 8 na Jamhuriyyar Ghana ta hudu. Ya samu nasara da kuri’u dubu goma sha biyar da dari bakwai da sittin da daya 15,761 wanda ya samu kashi hamsin da hudu da digo hamsin da daya 54.51% na jimillar kuri’u yayin da dan takarar majalisar dokokin kasar NDC Sadik Abubakar ya samu kuri’u dubu goma sha ukku da dari da hamsin da ukku 13,153 ya samu kashi arba'in da biyar da digo arba'in da tara 45.49% na kuri’u da dan takara mai zaman kansa Adom Douglas Kwakye ya samu kuri’u dubu goma sha daya da hamsin da biyu 11,052.[7][8]
A cikin shekarar, alif dubu biyu da ashirin da daya 2021, Adu tare da Alexander Kwamena Afenyo-Markin, Abdul-Aziz Ayaba Musah, Laadi Ayii Ayamba da Emmanuel Kwasi Bedzrah an rantsar da su yayin babban zama na shekarar, 2021 na Majalisar ECOWAS wanda ya faru a Freetown a Saliyo.[9]
Kwamitoci
gyara sasheAdu shine shugaban kwamitin matasa, wasanni da al'adu[10] kuma memba a kwamitin lafiya.[11][12][13]
Rigima
gyara sasheA cikin watan Afrilun shekara ta, dubu biyu da ashirin da bakwai 2017, Hukumar Burtaniya a Ghana ta zargi Adu, George Boakye, Richard Acheampong, da Joseph Benhazin Dahah da taimakawa 'yan uwansu shiga Burtaniya ba bisa ka'ida ba ta hanyar amfani da fasfo din diflomasiyya. Adu ya tafi Landan ne tare da matarsa da diyarsa kuma ana zargin ya bar su a baya a Biritaniya.[14][15][16][17]
Manazarta
gyara sashe- ↑ 1.0 1.1 1.2 "Parliament of Ghana". www.parliament.gh. Retrieved 2020-01-25.
- ↑ "Johnson Kwaku Adu retains Ahafo Ano South West seat for the third time". e.TVGhana (in Turanci). 2020-12-09. Retrieved 2022-02-04.
- ↑ 3.0 3.1 3.2 3.3 "Ghana MPs - MP Details - Adu, Johnson Kwaku". www.ghanamps.com. Retrieved 2020-01-25.
- ↑ "Members of Parliament". Fact Check Ghana (in Turanci). Retrieved 2022-02-04.
- ↑ Effah, Steven (2020-06-20). "Second round of NPP primaries begin across Ghana". 3NEWS. Archived from the original on 2023-06-02. Retrieved 2022-02-04.
- ↑ "#NPPDecides: Profiles of aspirants going unopposed in Ashanti Region". Citinewsroom - Comprehensive News in Ghana (in Turanci). 2020-06-20. Retrieved 2022-02-04.
- ↑ FM, Peace. "2020 Election - Ahafo Ano South West Constituency Results". Ghana Elections - Peace FM. Retrieved 2022-02-04.
- ↑ "Ahafo Ano South West – Election Data Center – The Ghana Report" (in Turanci). Retrieved 2022-02-04.
- ↑ author; ANAETO, Fred (2021-03-29). "1st Extraordinary Session 2021 of ECOWAS Parliament: Adoption of the Strategic Plan (2020-2024) as the first priority". ECOWAS Parliament Website (in Turanci). Retrieved 2022-02-04.
- ↑ "Hooliganism now a threat to Ghana's hosting rights for the 2023 All Africa Games". Modern Ghana (in Turanci). Retrieved 2022-02-04.
- ↑ "Parliament of Ghana". www.parliament.gh. Retrieved 2022-02-04.
- ↑ Amoah, Pascal Nii-Gogo (17 September 2021). "Appointment of next Black Stars coach should be based on merit, not color - Parliamentary Committee on Sports to GFA". Kickgh. Archived from the original on 3 June 2023. Retrieved 4 February 2022.
- ↑ Takyi, Christian. "NSA BOARD INAUGURATED". Ministry of Youth and Sports (in Turanci). Retrieved 2022-02-04.
- ↑ "U.K. Accuses 4 Ghanaian MPs of Visa Fraud". Face2Face Africa (in Turanci). 2017-04-28. Retrieved 2022-02-04.
- ↑ "Four MPs barred from the UK for 'visa fraud'". Citi 97.3 FM - Relevant Radio. Always (in Turanci). 2017-04-26. Retrieved 2022-02-04.
- ↑ Boakye-Yiadom, Nana; Searcey, Dionne (2017-04-27). "Britain Accuses Ghana Lawmakers of Visa Fraud". The New York Times (in Turanci). ISSN 0362-4331. Retrieved 2022-02-04.
- ↑ "4 MPs Busted For VIsa Fraud". DailyGuide Network (in Turanci). 2017-04-27. Retrieved 2022-02-04.