Zayyad Ibrahim

Dan siyasar Najeriya

Zayyad Ibrahim (an haife shi a shekara ta 1965) ɗan siyasan Najeriya ne. Ya taba zama dan majalisar tarayya mai wakiltar mazabar Igabi ta jihar Kaduna a majalisar wakilai ta 9, daga shekarun 2019 zuwa 2023. [1] [2]

Zayyad Ibrahim
mamba a majalisar wakilai ta Najeriya,

3 ga Yuli, 2019 -
District: Igabi
Rayuwa
Haihuwa Igabi, 22 ga Maris, 1965 (59 shekaru)
ƙasa Najeriya
Karatu
Harsuna Turanci
Pidgin na Najeriya
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa
Employers gwmanatin najeriya
Mamba Majalisar Wakilai (Najeriya)
Imani
Addini Musulunci
Jam'iyar siyasa All Progressives Congress

Rayuwar farko

gyara sashe

An haifi Zayyad Ibrahim a ranar 22 ga watan Maris 1965 kuma ɗan asalin jihar Kaduna ne. [3]

Aikin siyasa

gyara sashe

A zaɓen shekarar 2023, Ibrahim ya sake tsayawa takara a ƙarƙashin jam’iyyar All Progressives Congress amma abokin hamayyarsa Hussaini Muhammad Jallo na jam’iyyar Peoples Democratic Party ya doke shi. [4] [5]

Hon. Zayyad ya aiwatar da wani shiri, tare da haɗin gwiwar Rt. Hon. Yusuf Ibrahim Zailani, Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kaduna wanda kuma ya ninka matsayin Shugaban Majalisar Dattawan Arewa, don tallafa wa al’ummarsu da takin zamani da sama da Naira 30,000,000 don inganta rayuwarsu. [6]

Manazarta

gyara sashe
  1. "Citizen Science Nigeria". citizensciencenigeria.org (in Turanci). Retrieved 2024-12-10.
  2. "Hon. Zayyad impact on politics is second to none". SUB - SAHARA NEWS (in Turanci). 2021-07-12. Retrieved 2024-12-10.
  3. "Lawmakers - ConsTrack Track and Report on Governement Funded Projects in Nigeria". www.constrack.ng. Retrieved 2024-12-10.
  4. Ukoh, Emmanuel (2024-02-04). "Kaduna Re-run Election: APC, PDP Win Two Seats Each In 4 LGAs". Voice of Nigeria (in Turanci). Retrieved 2024-12-10.
  5. Igwe, Ignatius (2024-02-04). "APC, PDP Candidates Emerge Winners In Kaduna Bye-Election". Channels Television (in Turanci). Retrieved 2024-12-10.
  6. Sabiu, Muhammad (2023-01-22). "Kaduna lawmakers empower constituents with over N30m cash, fertilizer". Tribune Online (in Turanci). Retrieved 2024-12-10.