Zainab Usman ƙwararriyar masaniya ce kuma masaniyar manufofin jama'a a bankin duniya da ke Washington DC

Zainab Usman
Rayuwa
Haihuwa 1986 (37/38 shekaru)
Karatu
Makaranta Jami'ar Oxford Doctor of Philosophy (en) Fassara
University of Birmingham (en) Fassara Master of Science (en) Fassara
Jami'ar Ahmadu Bello Digiri a kimiyya
Harsuna Turanci
Faransanci
Hausa
Sana'a
Sana'a Mai tattala arziki
Employers Carnegie Endowment for International Peace (en) Fassara

Kwarewar nata ya shafi mulki da cibiyoyin kula da albarkatun ƙasa. A yanzu haka tana ofishin babban masanin tattalin arziki, Yankin Afirka a matsayin kwararriya, ta shiga bankin duniya a matsayinta na matashiyar kwararriya a fannonin zamantakewa, birane, kauyuka da juriya.

Ita ce marubuciya a wani littafi mai suna "Economic diversification in Nigeria: Fractious politics and economy beyond oil" ita ce mawallafiyar wata kasida a Jami'ar Oxford ta Burtaniya "Nasarar da Rashin nasarar sake fasalin tattalin arziki a sasanta rikicin siyasar Najeriya bayan soja"

Rayuwar farko da ilimi

gyara sashe

An haifi Zainab a Najeriya. Ta halarci makarantar sakandaren Therbow da ke Zariya, sannan kuma ta yi karatun digiri na farko a fannin kimiyya a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zariya (2008), sannan kuma ta yi karatun digiri na biyu (M.Sc.) a fannin tattalin arzikin kasa da kasa na siyasa daga jami'ar Birmingham UK (2011) da Doctor na falsafa (Ph.D) a cikin ci gaban duniya daga Jami'ar Oxford (2017).

Zainab Usman a yanzu haka tana aiki a bankin duniya, ofishin babbar masaniyar tattalin arziki, yankin Afirka a matsayinta na kwararriyar jama'a. Ta taba yin aiki a kungiyar tattalin arzikin yammacin Afirka (ECOWAS), Kungiyar Crises ta Duniya da Makarantar Gwamnati ta Blavatnik a Jami'ar Oxford. ta kuma nemi shawarwari kan ci gaban kasa da kasa (DFID), da kuma ofishin mai ba da shawara kan harkokin tsaro na kasa (ONSA). Ta rubuta wa CNN, Turanci na Al Jazeera, The Washington Post, tubar da kuma kafofin yada labarai na duniya. [1]

Manazarta

gyara sashe