Zaben gwamnonin Najeriya 2023
An gudanar da zaben gwamnonin Najeriya na 2023 na gwamnonin jihohi a jihohi 31 cikin 36 na Najeriya. A ranar 18 ga watan Maris,a daidai lokacin da aka gudanar da zaɓen kowace Majalisar Dokoki ta Jiha, makonni uku bayan zaben shugaban kasa da na ƴan majalisar dokoki - yayin da za a gudanar da zaɓen jihar Imo, da Kogi da Bayelsa a ranar 11 ga watan Nuwamba.[1][2][3][4] Zaɓen gwamnonin da aka saba yi na ƙarshe na dukkan jihohin kasar shi ne a shekarar 2019 . Dukkanin Jihohin dai na da wa’adi biyu na Gwamnoni wanda hakan ya sa gwamnoni 18 da ke kan karagar mulki ba za su iya sake tsayawa takara ba.
Iri | gubernatorial election (en) |
---|---|
Kwanan watan | 25 ga Janairu, 2024 |
Ƙasa | Najeriya |
Sakamako
gyara sasheKafin zaɓen dai akwai gwamnonin APC 21, gwamnoni 14 na PDP, da na APGA guda ɗaya. Daga cikin ofisoshin gwamnan da za a yi zaɓe a shekarar 2023, 19 na ɗan jam’iyyar APC ne, yayin da 12 kuma ɗan PDP ne ke riƙe da shi.
Manazarta
gyara sashe- ↑ Oyekanmi, Rotimi (26 February 2022). "It's Official: 2023 Presidential, National Assembly Elections to Hold Feb 25 ". INEC News. Retrieved 27 February 2022.
- ↑ Jimoh, Abbas (26 February 2022). "INEC Sets New Dates For 2023 General Elections". Daily Trust. Retrieved 26 February 2022.
- ↑ "INEC shifts governorship, assembly polls by one week". The Punch. Retrieved 9 March 2023.
- ↑ Adenekan, Samson. "INEC releases date for Bayelsa, Imo, Kogi off-cycle governorship elections". Premium Times. Retrieved 25 October 2022.