Yusuf Mohamed Ismail ( Somali , Larabci: يوسف محمد إسماعيل‎ ‎ 11 Satumba 1960 – 27 Maris 2015), wanda aka fi sani da Bari-Bari, ɗan siyasan Somaliya ne kuma jami'in diflomasiyya . Ya shiga ayyukan diflomasiyya a shekarata 2007. A lokacin mutuwarsa, ya kasance Ambasada a ƙasar Switzerland kuma Wakilin Dindindin a Majalisar Ɗinkin Duniya a Geneva tun daga 4 Afrilun shekarar 2008.

Yusuf Mohamed Ismail
Rayuwa
Haihuwa Garowe (en) Fassara, 11 Satumba 1960
ƙasa Somaliya
Mutuwa Mogadishu, 27 ga Maris, 2015
Yanayin mutuwa kisan kai
Karatu
Makaranta University of Bologna (en) Fassara
Sana'a
Sana'a Mai wanzar da zaman lafiya da ɗan siyasa
Imani
Addini Musulunci
Jam'iyar siyasa independent politician (en) Fassara
Yusuf Mohamed Ismail

Farkon rayuwa

gyara sashe

An haifi Ismail a Bologna, Italiya zuwa ga ahalin musulmin Somaliya masu kishin addini.[1] Yayi karatu a Jami'ar Bologna . Yayi aure kuma yana da yara.

A ranar 27 ga Maris din shekarar 2015, Ismail ya ji rauni a wani harin da mayakan al-Shabaab suka kai a otal din Makka al-Mukarama da ke Mogadishu yayin halartar wani taro. Daga baya ya mutu daga rauni da ya ji a asibiti, yana da shekara 54. An binne shi a Garoowe, Puntland a ranar 29 ga Maris.

Manazarta

gyara sashe
  1. "Somalia. Attacco al-Shabaab in un hotel a Mogadiscio, almeno 13 morti". ArticoloTre. 27 March 2015. Archived from the original on 4 March 2016. Retrieved 6 April 2015.

Hanyoyin haɗin waje

gyara sashe