Yusuf Datti Baba-Ahmed
Yusuf Datti Baba-Ahmed Sanata, ne, kuma dan kasuwa, sannan kuma dan kasar nigeria.wanda ya kafa jami'ar Baze. Ya kasance mutum ne wanda ba ya bukatar wata doguwar gabatar wa. Sunansa ya yi amo, yin zarra, da kuma yin fice a sassa daban-daban na rayuwar al’umma ta yau da kullum.[1]
Yusuf Datti Baba-Ahmed | |||
---|---|---|---|
| |||
Rayuwa | |||
ƙasa | Najeriya | ||
Sana'a | |||
Sana'a | ɗan siyasa | ||
Imani | |||
Jam'iyar siyasa | Congress for Progressive Change (en) |
Farkon Rayuwa da Karatu
gyara sasheBaba-Ahmed, dan asalin yankin Tudun Wada ne da ke cikin kwaryar Birnin Zariya ta Jihar Kaduna. An haife shi shekaru 45 da suka gabata a garin na zariya dai-dai da ranar 29 ga watan Junairun shekarar alif Dari tara da sittin da tara (1969). Gabanin tsundumarsa a fagen neman ilimin zamani sai da ya soma da neman ilimin addinin Musulunci a shekarun farko-farko na kuruciyarsa, wannan ya zo dai-dai da tsarin tarbiya irin ta ‘ya’yan Musulmi na bude idanu da neman ilimin kadaita Mahalicci tare da sanin fikihu na Farlu-Ainni. A bangaren ilimin zamani kuwa, Datti ya bi matattakalar neman ilimi tun daga mataki na farko har sai da ya dangane da digirin-digirgir.
Bayan kamala karatunsa na Sakandare a Makarantar Sakandare ta Rundunar Sojojin sama da ke Jos ta Jihar Filato, tare da samun sakamako mai kyawo a jarabawarsa ta GCE a shekarar alif 1986, Datti ya samu gurbin karatu a jami'ar Maiduguri domin karantar fannin Tsimi da Tanadi (wato Economics), inda ya kamala tare da samun shaidar digirin farko a wannan fannin a shekarar alif 1992.
A fagen neman ilimi kuwa, ya yada shi a tsakanin al’umma, ya kafa muhimmin abin tarihi a duniyar ilimi domin yanzu haka yana da mallakin mabambantan takardun shaidar digiri dai-dai har guda hudu jere da juna, a cikinsu kuwa har da digirin digirgir a fannin tsimi da tanadi, don haka gagarumar gudummawar da ya bayar a jiya da wacce ya ke bayarwa a yau ga ci-gaban ilimi al’amari ne da zai yi wuya a misalta shi.
Siyasa da Kasuwanci
gyara sasheA fagen shugabanci da siyasa kuwa fitaccen jagora na siyasa, tarihin da ya kafa na gudanar da wakilcin jama’a a majalisar wakilai da kuma majalisar dattawa ta tarayyar Najeriya sun sanya shi a wani muhimmin gurbi wanda ya zamo abin kwatance a tsakanin ‘yan siyasarmu na yau, wanda dalili kenan da ya sa har zuwa yau din nan hasken tauraruwar tasiri da kimarsa ba ta taba dushewa ba.
Ta fuskar kasuwanci kuwa, hamshakin dan kasuwa ne wanda ya san kabli da ba’adin kasuwanci. Zaka yarda da hakan idan ka yi duba ga irin gudummawarsa ga habaka harkokin kasuwanci da na tattalin arziki wanda har ya zama abin kwatance da alfahari ga al’umma.
Bayan aikin bautar kasa da ya yi a jami’ar Aikin gona ta Abeokuta dake Jihar Ogun a tsakanin shekarun alif 1992 zuwa shekarar alif 1993, Baba-Ahmed ya sake komawa a jami’ar ta Maiduguri domin karatun digirinsa na biyu a fannin na tsimi da tanadi wanda ya samu nasarar kammalawa a shekarar alif 1995.
Daga nan sai likkafar neman iliminsa ta yi gaba inda ya keta hazo zuwa shahararriyar jami’ar nan ta Wales, da ke Birtaniya, (wato University of Wales, Cardiff), inda ya samu karin digiri na uku a fannin harkokin gudanarda hada-hadar kasuwanci, wato MBA a shekarar alif 1996.
Haka ma bayan wasu ‘yan shekaru na hidimomin kasuwanci da yiwa jama’a hidima, Datti ya sake komawa Nahiyar Turai domin kara zurfafa iliminsa, a wannan karon kuwa jami’ar nan ta Wesminster da ke Birnin London ita ya yiwa tsinke, wato University of Wseminster, London, inda ya kamala da samun digirin-digirgir wato PHD, a shekarar 2006.
Sauran karance-karancen ilimi da kuma kwasa-kwasan da wannan matashin dan boko ya halarta sun hada da wata takardar shaidar Difiloma a fannin tattarawa tare da adana bayanai wadda ya samu a shekarar 1993. Sai kuma wata takardar shaida akan dubarun tabbatar da dai-daito da kwatanta gaskiya, wacce ya samu daga cibiyar tuntuba ta Arbitrage Consulting a shekarar 1996. Daga nan kuma sai wata takardar shaida akan aiwatar da harkokin Tsimi da Tanadi da ya samu daga Makarantar Koyar da harkokin Tsimi da Tanadi ta Birnin Landan, wato London School for Practican Economics a shekarar 1998.
A bangaren aikace-aikace kuwa, ko bayan aikin da ya yi a Jami’ar Aikin Gona ta Abeukuta a tsakanin shekarun 1992 zuwa shekarar alif 1993, a lokacin da yake aikin hidimar Baba-Ahmed ya taba rike mukamin Kodinatan ayyuka na Cibiyar Bincike da Aikin Tattara Bayanai ta Baze Research and Data Service, tun daga watan Mayun shekarar 1993 zuwa watan Satumbar shekarar alif 1994, sa’annan daga watan Oktoban shekarar alif 1994 zuwa Satumbar shekarar alif 1995.
Haka kuma Sanata Datti ya rike mukamin Jami’i na biyu a Ma’aikatar Buga Takardun Kudi da sauran Muhimman Takardu ta Kasa, wato NSPMC da ke Victoria Island a Birnin Legas. Ya taba zama Jami’in gudanar da harkokin Banki a reshin Bankin First Bank da ke Birnin Landan daga watan Yulin shekarar 1997 zuwa watan Disambar shekarar 1998, da kuma tsakanin watan Disambar shekarar 1998 zuwa watan Mayun shekarar 1999. Kuma Sanata Datti ya rike mukamin Jami’in gudanarwa na Kamfanin Billfinger+ Berger Limited, da ke Landan. Datti Baba-Ahmed ya sake komawa Cibiyar Bincike da Tattara Bayanai ta Baze a shekarar 1999 zuwa shekarar 2003 da kuma shekarar 2007 zuwa shekarar 2008, inda ya rike matsayin Manajan Daraktan Cibiyar ta gudanar da bincike. [2]
A fagen Siyasa kuma Baba-Ahmed, mutum ne da tun tashinsa ya kasance mai cudanya da mu’amalar kirki da jama’arsa, domin haka kamar salon maganar nan ne da Hausawa ke cewa, ko da iska ya zo, ya tarar da kaba ta na rawa, koda siyasa ta zo ta tarar da Datti cikin jama’a, ba wai siyasar ce ta kawo shi cikin jama’a ba.
Baba-Ahmed ya taba zama Dan Majalisar mai Wakiltar Al’ummar Mazabar Zariya a Majalisar Wakilai ta Tarayya daga shekarar 2003 zuwa shekarar 2007. Haka kuma a tsakanin shekarar 2011 zuwa shekarar 2012 ya wakilci Al’ummar mazabar Dan Majalisar Dattawa ta Kaduna ta Arewa a Majalisar Dattawa ta Kasa. Datti Baba-Ahmed, Sanannen Dan kishin Kasa ne, mai cike da muradin taimakawa al’umma, kuma mutum ne da ya aiwatar da tarin ayyukan taimako da jinkayin jama’a a fannonin rayuwar al’umma daban-daban, tun ma dai ba a fagen Ilimi ba.
Taimako (Aikin jinkai)
gyara sasheBaba-Ahmed, a kashin kansa ya gina tare da bayar da kyautar makarantun karamar Sakandare har guda biyu ga Al’ummar mahaifarsa ta Zariya. Makarantun masu daukar sama da dalibai 4,000, wadanda Shugaban Kasa Janar Muhammadu Buhari ya kadammar da daya a watan Fabrairun shekarar 2005, tun kamin ya sake zama shugaban Kasa. Haka kuma Mai Martaba Sarkin Zazzau Alhaji Dakta Shehu Idris ya kaddamar da daya a watan Disambar shekarar 2006. Wadannan makarantu, yanzu haka sun yaye sama da dalibai 12,000 daga sassa daban-daban na Birnin Zariya da kewaye. Kuma ko bayan wannan a duk shekara ya kan samar da tallafin karatu ga daruruwan matasa ta hanyar sayowa tare da rarraba takardun cikewa na karatun Difiloma da Digiri da kuma na jarabawar NECO da WAEC da kuma JAMB/UTME kyauta ga al’umma. Kuma a wani bangare na gudummawarsa ga addini da kuma yada shi, a shekarar 2006, Sanata Yusuf Datti ya samar da masalacin Juma’a na AR-RAHMA kyauta ga al’ummar yankin Jabi.
A shekarar 2008 ne Baba-Ahmed ya kafa wani muhimmin abin tarihi da ba a taba ganin irinsa a fagen ilimi a kafatanin Arewacin Nigeriya ba, a inda a watan Yulin shekarar 2014 ne a kashin kansa ya kirkiro tare da samar da Jami’a mai zaman kanta wadda aka fi sani da Jami'ar Baze (wato BAZE UNIVERSITY) da ke da mazauninta a Abuja, Babban Birnin Tarayyar Nijeriya. [3]
A lokacin bukin bude wannan makarantar ta BAZE UNIVERSITY manyan shuwagabanin Najeriya, da Sarakunan Najeriya zuwa ga manyan masana na Najeriya duk sun halarci taron, kuma sun yaba sun jinjina da wannan namijin kokarin da Datti Baba-Ahmed ya yin a kafa makarantar. Daga cikinsu akwai Mataimakin Shugaban Kasa na wancan lokacin Namandi Sambo, Sarkin Zazzau Alhaji Shehu Idris, Gwamnan Baban Bankin Najeriya na wancan lokacin Sarkin Kano Muhammad Sanusi II. Haka akwai Ibrahim Badamasi Babangida, tsohon shugaban kasa, Sanata David Mark shugaban Majalisar Dattawa na wancan lokacin. Shehu Aliyu Shagari, Yakubu Gawon, da sauran wasu muhimman mutane da shuwagabanin Kasar Najeriya. Jami’ar wadda tun kafuwarta har zuwa yanzu shine ke rike da matsayin uban Jami’ar, wato Pro-Chancellor, Jami’a ce da ta yi matukar fice tare da yin zarra a fagen ilimi da bincike-bincike a tsakanin manyan jami’o’in Kasar nan. [4]
Yanzu haka dai ko bayan matsayin uban Jami’ar ta Baze da yake rike da shi tun kafuwarta har zuwa yau Datti Baba-Ahmed shi ne manajan Daraktan Cibiyar Bincike-Bincike da Aikin Tattara Bayanai ta Baze Research and Data Services Limited. Kuma shine shugaban Kamfanin gine-gine na Baze Construction Limited, kamfanin da yanzu haka ya samar da kafar neman abin jefawa a baka ga mutane da dama sama da mutum 300, ciki kuwa har da fararen fata ‘yan kasashen waje. Datti Baba-Ahmed ya sha samun karramawa da lambobin yabo masu tarin yawa saboda yabawa da kwazonsa da kuma namijin kokarinsa tare da dimbin gudummawarsa ga ci-gaban al’umma ta fannoni da dama. Yanzu haka yana da lambar FSAN ta kungiyar Masana Kimiyya ta Kasa. [5]
Sa’annan kuma shine uban kulub din masu wasan kwallon Polo ta Zariya, wato, Zaria Polo Club tun daga shekarar 2007 har zuwa yau dinnan. Kuma har wayau shine shugaban Dandalin Sabuntawa da Kyautata Al’amurran jama’a na Renaisssance Forum For Sociatal Reforms. Za a iya cewa, Sanata Yusuf Baba-Ahmed mutum ne da ke matukar sha’awar harkokin wasanni musamman wasannin squash da Chess, haka kuma yana da sha’awa ga harkokin muhawarori na ilimi.
Manazarta
gyara sashe- ↑ https://businessday.ng/politics/article/who-is-yusuf-baba-ahmed-peter-obis-running-mate/
- ↑ https://businessday.ng/politics/article/who-is-yusuf-baba-ahmed-peter-obis-running-mate/
- ↑ https://dailytrust.com/tag/yusuf-datti-baba-ahmed/
- ↑ https://www.vanguardngr.com/2023/03/my-brother-senator-dr-yusuf-datti-baba-ahmed/
- ↑ https://labourparty.com.ng/yusuf-datti-baba-ahmed/