Yaryasa

mazaɓa a jihar Kano, Najeriya

MYaryasa gari ne dake a ƙaramar hukumar Tudun Wada a Jihar Kano. Yaryasa na daga cikin Mazaba Goma sha ɗaya na ƙaramar hukumar Tudun Wada.[1][2]

Yaryasa
gunduma ce a Najeriya
Bayanai
Ƙasa Najeriya
Wuri
Map
 11°17′13″N 8°18′39″E / 11.28695°N 8.31093°E / 11.28695; 8.31093
Ƴantacciyar ƙasaNajeriya
Jihohin Najeriyajihar Kano
Ƙananan hukumumin a NijeriyaTudun Wada
Kofar garin Yaryasa

Garin Yaryasa yana kan Titin Jos Wanda ya taso daga Kwanar Dan Gora.

Suna'ar mutanen garin yaryasa

gyara sashe

Mutanen garin yaryasa sun ta allakane akan noma, kasuwanci da kamun kifi da ma'aikatan gwamnati da yan siyasa.

Noman rani Dana damina shine babbar hanyar da suka dogara dashi, suna noma Masara, dawa, shinkafa, rake, Tumatir, albasa, kubewa, Tafarnuwa, dadai sauran Kayan Amfanin gona. Sannan akwai ma'adanai, dasuke tona daga rafikan dasuke zagaye dasu, ma'adanai sune kwallin kura,

Makarantun Garin

gyara sashe

Sannan garin yaryasa yana ɗauke da makarantun zamani akwai firamare Guda hudu Acikin garin yaryasa, Sakandire ta maza ƙarama da babba, sakandire ta yan mata ƙarama da babba.

Tattalin Arziki

gyara sashe

Garin yaryasa Yanada Arzikin kifi sakamakon yawan Rafuka da suke dashi. Sannan suna da babbar kasuwar siye da siyar da kifi danye,soyayye, da kuma gasashshe. Akwai kuma kasuwar sayar da kayan gwari wanda ake ɗauka akai Kudancin Najeriya. kamar Legas,Ibadan da warri

Manazarta

gyara sashe
  1. https://www.manpower.com.ng/places/wards-in-lga/447/tudun-wada
  2. https://mapcarta.com/31170670