Wahab Dosunmu
Wahab Dosunmu (ranar 14 ga watan Mayun 1939 - ranar 9 ga watan Yunin 2013) ɗan siyasar Najeriya ne, ya kasance ministan ayyuka da gidaje a jamhuriya ta biyu ta Najeriya.[1] Ya kasance ɗan majalisar dattawan Najeriya daga shekarar 1999 zuwa 2003. Dosunmu ya tsaya takarar gwamnan jihar Legas a 1999 amma ya sha kaye a hannun Sanata Bola Tinubu. Ya lashe kujerar Sanatan Legas ta Yamma a kan dandalin Alliance for Democracy (AD). Daga baya, ya sauya sheƙa tare da wasu ƴan majalisar tarayya na AD zuwa jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP).[2]
Wahab Dosunmu | |
---|---|
mutum | |
Bayanai | |
Bangare na | Nigerian senators of the 4th National Assembly (en) |
Jinsi | namiji |
Ƙasar asali | Najeriya |
Lokacin mutuwa | 9 ga Yuni, 2013 |
Sana'a | ɗan siyasa |
Muƙamin da ya riƙe | mamba a majalisar dattijai ta Najeriya |
Ɗan bangaren siyasa | Alliance for Democracy (en) |
Dosunmu ya ci gaba da zama ɗan majalisar dattawa mai fafatuka inda ya kasance shugaban kwamitin majalisar dattawa kan kimiya da fasaha har zuwa cikin shekarar 2003. Daga baya ya sauya sheƙa zuwa jam'iyyar People's Democratic Party daga tsohuwar jam'iyyarsa ta Alliance for Democracy. A cikin shekarun 1990, ya yi fice a fafutukar naɗa wanda ake kyautata zaton shi ne ya lashe zaɓen shugaban ƙasa na ranar 12 ga watan Yunin 1993, MKO Abiola. Ya kasance Babban Kwamishinan Malesiya tsakanin shekarar 2004 zuwa 2007. Ya mutu a ranar 9 ga watan Yunin 2013, a Amurka yana da shekaru 74.
Ɗan gwagwarmayar siyasa
gyara sasheDr Wahab Dosunmu, ɗan gwagwarmayar siyasa ne kuma jigo a jam'iyyar National Democratic Coalition (NADECO)
Marigayi ɗan siyasar yana daya daga cikin waɗanda suka yi fafutukar ganin an tabbatar da wa'adin shugabancin marigayi Cif MKO Abiola a ranar 12 ga watan Yunin 1993 ta hannun NADECO.[3]
Manazarta
gyara sashe- "Tinubu, Wasu Suna Tafi Don Gwajin Sahihanci", Labaran PM, Disamba 18, 1998