Alliance for Democracy (Nijeriya)

Jam'iyyar siyasa a Nijeriya

Alliance for Democracy jam'iyyar adawa ce a Najeriya. An kafa ta ranar 9 ga watan Satumba, 1998. A zaɓen ƴan majalisu na shekarar 2003, a ranar 12 ga Afrilun shekarar 2003, jam'iyyar ta samu kashi 8.8% na yawan kuri'un jama'a da kujeru 34 cikin 360 na ' yan majalisar wakilan Najeriya da kujeru 18 cikin 109 na majalisar dattawan Najeriya.[1] An kafa jam’iyyar ne domin tallata manufar kabilar Yarbawa a tarayyar Najeriya biyo bayan soke zaɓen shugaban ƙasa da aka gudanar, na ranar 12 ga watan Yunin 1993 da aka yi imanin cewa Cif MKO Abiola, wani hamshakin attajiri ɗan ƙabilar Yarbawa ne ya lashe zaɓen.[2]

Alliance for Democracy
Bayanai
Iri jam'iyyar siyasa
Ƙasa Najeriya
Ideology (en) Fassara progressivism (en) Fassara
Mulki
Hedkwata Abuja
Tarihi
Ƙirƙira 9 Satumba 1998

A shekarar 2007 Cif Dr. Christopher Pere Ajuwa, na yankin Neja Delta, ya yi takara amma ya sha kaye, a takarar neman kujerar shugaban Najeriya.[3][4]

Rikici gyara sashe

Jam’iyyar ta yi takun saka tsakanin Mojisola Akinfenwa da Adebisi Akande, inda har zuwa watan Satumban 2006, ɓangaren ƴan Bisi Akande yai maja da wasu jam’iyyun adawa suka kafa jam’iyyar Action Congress.[5]

Manufa da Maƙasudi gyara sashe

Jam'iyyar na shirin gabatar da abubuwa kamar haka:

  • Ilimi kyauta;
  • Shirin kula da lafiya kyauta;
  • Hadaddiyar ci gaban karkara;
  • Cikakken aiki

Manazarta gyara sashe

  1. "Alliance for Democracy | Post-Independence Nigerian Party Politics". Nigerian Scholars (in Turanci). Retrieved 2022-09-05.
  2. "Alliance For Democracy (AD) [Nigeria 4th Republic] — StudyHQ.net" (in Turanci). 2021-01-22. Retrieved 2022-09-05.
  3. "Our Campaigns - Candidate - Christopher Pere Ajuwa".
  4. "Our Campaigns - Political Party - Alliance for Democracy (AD)".
  5. "Alliance for Democracy | Post-Independence Nigerian Party Politics". Nigerian Scholars (in Turanci). Retrieved 2022-09-05.

Hanyoyin haɗi na waje gyara sashe