Victoria Adaobi Obasi (an haife ta a ranar 14 ga watan Afrilu 1952)[1] Ita ce babbar mataimakiyar shugaban jami'ar jihar Imo na yanzu.[2][3] Ta fito daga Ogboko dake ƙaramar hukumar Ideato ta kudu a jihar Imo Najeriya.[4] Tsakanin shekarun 2011-2013, ta kasance kwamishiniyar ilimi a jihar Imo.[4][5][6][7]

Victoria Adaobi Obasi
Rayuwa
Haihuwa Najeriya, 14 ga Afirilu, 1952 (72 shekaru)
ƙasa Najeriya
Harshen uwa Harshen, Ibo
Karatu
Makaranta University of Hull (en) Fassara Digiri a kimiyya : zoology
University of Hull (en) Fassara Master of Science (en) Fassara
Alvan Ikoku Federal College of Education (en) Fassara
University of Hull (en) Fassara Doctor of Philosophy (en) Fassara
Harsuna Turanci
Pidgin na Najeriya
Harshen, Ibo
Sana'a
Sana'a Malami
Employers Jami'ar jihar Imo

Rayuwar farko, ilimi da aure

gyara sashe

Victoria Adaobi Obasi diyar Cif Fred da Ezinne Felicia Nnoham. Obasi ta fara karatunta na farko a Holy Rosary Primary School, Oguta sannan ta wuce Holy Rosary Secondary, Ihioma. Ta kuma halarci Kwalejin Ilimi ta Tarayya ta Alvan Ikoku, Owerri. Obasi ta sami digiri na farko (1984), masters' (1985) da digiri na uku (1989) daga Jami'ar Hull, Ingila. Ta yi hidimar ƙasa ta matasa a kwalejin horar da mata, Enugu (1980). Adaobi ta auri Cif Charles Obasi na Dim Na Nume a ƙaramar hukumar Isu ta jihar Imo kuma tana da ‘ya’ya biyar.[4]

Ta ci lambar yabo ta Bursary Award for Excellence, Jami'ar Hull sau uku a jere a shekarun 1987,1988 da 1989.[8]

Wallafe-wallafe

gyara sashe

Ta rubuta littattafai biyar, ciki har da The implementation of continuous assessment in secondary schools in Imo State, Nigeria,[9] da kuma wallafa muƙaloli da mujallu a cikin mujallu na duniya.

Ta kasance memba na ƙwararrun ƙungiyoyi a Najeriya irin su Cibiyar Ilimi ta Najeriya, Ƙungiyar Kula da Manhaja ta Najeriya (CON), da kuma a wasu ƙasashe kamar Kwalejin Preceptor Ingila (CPE) da Majalisar Ɗinkin Duniya na Curriculum da Instruction (WCCI).[10]

Manazarta

gyara sashe
  1. "Happy Birthday To Our Dear Honourable Chancellor, Imo State University, Owerri (Prof. Mrs. Victoria Adaobi Obasi)". www.imsugist.com. Retrieved 25 April 2018.
  2. "Imo State University Appoints A New Substansive VC. — Nigeria Today". www.nigeriatoday.ng. Archived from the original on 9 April 2018. Retrieved 8 April 2018.
  3. "IMSU Vice Chancellor, Prof Adaobi Obasi loses son – Punch Newspapers". www.punchng.com. 14 August 2017. Retrieved 25 April 2018.
  4. 4.0 4.1 4.2 "PROFILE OF PROF. MRS. VICTORIA ADAOBI OBASI" (PDF). Archived from the original (PDF) on 2017-08-29.
  5. "SPOTLIGHT ON PROF. VICTORIA ADAOBI OBASI". Archived from the original on 2023-02-08. Retrieved 2023-12-30.
  6. "Speakers biography - University of Skövde". www.his.se (in Turanci). Archived from the original on 20 August 2016. Retrieved 11 May 2018.
  7. "IMSU gets new Deputy Vice Chancellors". Retrieved 11 May 2018.[permanent dead link]
  8. "SPOTLIGHT ON PROF. VICTORIA ADAOBI OBASI". Arise Afrika. Archived from the original on 28 April 2018. Retrieved 11 May 2018.
  9. Adaobi, Obasi, Victoria (1989). The implementation of continuous assessment in secondary schools in Imo State, Nigeria (Thesis) (in Turanci). The University of Hull. Retrieved 11 May 2018.
  10. Nwafor (2020-01-12). "Prof Victoria Obasi: Proving her mettle in a man's world". Vanguard News (in Turanci). Retrieved 2022-08-11.