Ummu Ammara (Nusaibah bint Ka'ab)
Nusaybah bint Ka'ab ( Larabci: نسيبة بنت كعب ; Hakanan ʾUmm ʿAmmarah, Ummu Umara, Ummu marah [1] ) tana ɗaya daga cikin matan farko da suka musulunta. Tana ɗaya daga cikin sahabban Annabi Muhammad (S A W) .
Ummu Ammara (Nusaibah bint Ka'ab) | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | Madinah, |
Mutuwa | 634 |
Makwanci | Al-Baqi' |
Ƴan uwa | |
Abokiyar zama |
Zaid bin 'Asim Mazni (en) Ghaziyya ibn Amr al-Ansarí (en) |
Yara | |
Karatu | |
Harsuna | Larabci |
Sana'a | |
Mahalarcin
| |
Aikin soja | |
Ya faɗaci |
Yaƙin Uhudu Yaƙe -yaƙe Ridda Invasion of Banu Qurayza (en) Yaƙin Khaybar yaƙin Hunayn Yakin Yamama |
Imani | |
Addini | Musulunci |
Tarihi
gyara sasheTana cikin ƙabilar Banu Najjar da ke zaune a Madina, Nusaybah 'yar'uwar Abdullah bin K'ab ce, kuma mahaifiyar Abdullah da Habib ibn Zayd al-Ansari.[1]
Lokacin da shugabanni, jarumai, da masu fada aji na Madina su 74 suka sauka a al-Aqabah don yin rantsuwar yin biyayya ga addinin Islama biyo bayan koyarwar sabon addinin da Mus`ab ibn `Umair ya yi a garin, Nusaybah da Umm Munee Asma bint ʿAmr bin ' Adi su kadai ne mata biyu da suka yi mubaya'a kai tsaye ga Annabi Muhammadu (S A W) . Mijin na karshen, Ghazyah bin ʿAmr, ya kuma sanar da Muhammad cewa matan ma suna so suyi mubaya'a da kansu, kuma ya yarda. [1] Ta koma Madina ta fara koyar da matan garin addinin Musulunci. Wannan mubaya'ah ko jinginar ita ce a zahiri ta ba da mulki ga Muhammad a kan birni, ta hanyar manyan jiga-jiganta. Matsayinta mafi shahara shi ne a yakin Uhudu, inda ta kare annabi. Ta kuma halarci yaƙin Hunain, Yamamah da Yarjejeniyar Hudaybia .
Rayuwar ta
gyara sashe'Ya'yanta maza biyu, wadanda daga baya suka yi shahada a yakin, sun kasance ne daga aurenta na farko da Zaid bin ʿAsim Mazni. Daga baya ta auri bin ʿAmr, kuma ta haifi ɗa Tameem da ɗiya Khawlah. [1]
Manazarta
gyara sashe