Smshika
Barka da zuwa!
gyara sasheBarka da zuwa Hausa Wikipedia, Sadammuhammad11234! Mun ji daɗin gudummuwarku. Kuma ina fatan zaku tsaya ku ci gaba da bada gudummuwa. Anan ƙasa ga wasu shafuka da zasu taimaka wajen fahimtar Hausa Wikipedia da yadda ake gyara ta:
- Gabatarwa
- Tutorial
- Cheatsheet
- Yadda ake rubuta muƙala
- Manufofin Hausa Wikipedia
- Shawarwari goma akan gyaran Wikipedia
Zaku iya yin sayinin rubutunku idan kuna akan shafukan tattaunawa ta hanyar alamar tilde guda huɗu, kamar haka (~~~~); yin hakan, zaisa sunanku da cikkaken kwanan wata. In kana buƙatar wani taimako, ku duba Wikipedia:Tutorial, ko kuma ka tambayeni a . Na gode.Em-mustapha talk 15:58, 11 Satumba 2021 (UTC)
Hatsarin dumamar yanayi
gyara sasheAsalam @Sadammuhammad11234, da fatan kana lafiya. Wannan mukalar Hatsarin dumamar yanayi tana dauke da gyrarraki da dama ta yadda ba a iya fahimtar ta yadda ya dace. Saboda haka tana bukatan a inganta ta matuka. Musamman tunda kai ka fassara ta ya kamata ace ka kwatanta ta da ainihin mukalar ta Turanci. Zamuyi mata alamar gogewa sannan zuwa wani dan lokaci idan ba'a gyara ba zamu goge shafin. Nagode
Patroller>> 08:00, 14 Satumba 2023 (UTC)
- wslm, nagode, sosai admin zanyi kokari na kara ingatata daidai yanda zan eya Sadammuhammad11234 (talk) 10:11, 14 Satumba 2023 (UTC)
Lura da Fassara (Musamman na taken mukalai)
gyara sasheAslm @Sadammuhammad11234.. Dan AlLah a rika lura da take (title) na shafuka ta yadda zasu bada ma'ana. Taken wannan shafin Yanayin yanayin duniya wanda a Turance Global surface temperature ba yi ba - Yanayin bisashe na Duniya ko Yanayin wurare na duniya... Patroller>> 08:18, 14 Satumba 2023 (UTC)
- Wslm admin enah godeya zan dinga lura daedae gwargwadon yanda zan eya Sadammuhammad11234 (talk) 10:13, 14 Satumba 2023 (UTC)
saka bayanai akan mukalar "Monty Noble"
gyara sashe@Sadammuhammad11234, barka da safiya.. naga kaine ka kirkira mukalar Monty Noble, amma baka rubuta komai acikinta ba, yakamata mu ringa kokarin inganta ayyukanmu.Saifullahi AS (talk) 05:29, 17 Nuwamba, 2023 (UTC)
Neman Qarin Bayani
gyara sasheAssalamu alaykum @Smshika. Naga ka goge mini edits nawa dana yi a shafin Kudancin Ostiraliya, wanda bansan dalilin yin hakan ba. Da nayi nisa da yin edits din, amma yanzun ka mayar mini dashi farko. Don Allah ko zan iya sanin wannan dalilin ko kuskure kayi? @Uncle Bash007 na gode da saka templates da kayi. Amma kuma bansan ko kasan dalili undoing na edits na da @Smshika yayi ba.
Nagode.
Yahuzaishat (talk) 06:18, 4 ga Janairu, 2024 (UTC)
- Wa`alaikumu salam @Yahuzaishat ni ba admin ba tayaya zan gogema muƙalanka, ? Smshika (talk) 07:27, 4 ga Janairu, 2024 (UTC)
- Just seeing this. Hope you have sorted the issue. Share the page so that I can confirm the issue.
- best Patroller>> 12:54, 17 ga Afirilu, 2024 (UTC)
Gogewa
gyara sasheBarka da aiki @Smshika, naga kana ƙirƙirar maƙaloli na Disambiguation wanda ba maƙalolin Wikipedia ne ba. Su wadannan mahaɗu ne da suka haɗa Shafukan Wikipedia masu kamceceniya da suna ɗaya. Duba ƙarin bayani a Nan. Ka sani ana kirkirar irin wadannan shafukan ne kaɗai idan ya kasance akwai shafukan Wikipedia masu kamceceniyar suna. Sabo da haka zan goge dukkan shafukan mahaɗa wato Disambiguation Page da ka ƙirƙira ba bisa ka'ida ba. Nagode Gwanki(Yi Min Magana) 10:09, 23 ga Faburairu, 2024 (UTC)
Gyara
gyara sasheAslm, @Smshika, muna jin dadin irin gudunmawar da ka ke bayarwa, sai dai wani hanzari ba gudu ba makalolin ka na bukatar Gyara sosai. Ya kamata mu riƙa inganta duk makalar da muka fassara ko kirkira sannan ba ka saka masu Manazarta wanda hakan shima ya dace a saka, kasancewar idan aka fassara makala kusan Manazarta copying kawai za ayi daga inda aka fassarota ba wai sai an sha wahalar neman madogara ba.
Na bi ayyukan ka a tsanake kuma lallai akwai bukatar ka inganta aikin ka musamman irin rukunin aikin ka na fannin Yaruka da ka ke fassarawa na da raunin da suke buƙatar gyara matuka (kasancewar makalar da ta shafi yare/harshe na da SARƘAƘIYA KWARAI, la'akari da wasu kalmomi bamu da su a Hausa ko da akwai lallai suna da wahalar juyawa idan kuma mun juya su ɗin a Hausa to fa marasa zurfin tunani ba lallai su fahimci mi ake nufi ba) don fahimtar mi ake nufi. BnHamid (talk) 08:50, 4 ga Yuli, 2024 (UTC)
- Nagode sosai da gyran da kayinmin yallabai @BnHamid ammah wadanan muƙalolin da na ƙirƙira na yaruku sun woce wata biyu da na ƙirƙire su sbd lokacin munayin wata gasar ne koma a lokacin @Gwanki yayinmin magana na gyra yanzu yau na ƙirƙira wasu ko kaga kuskure a cikinsu? Smshika (talk) 09:20, 4 ga Yuli, 2024 (UTC)
- Manufar duk wata GASA shine a kawo cigaba bawai don kawai a faranta ran waɗanda suka samu nasarar lashe gasar ba. Hakan na nufin bai kamata mu mance da muhimmanci wannan farfajiya ba (abin nufi anan kar burin samun rabo a gasar da muke yi, ya saka mu yi wa Hausa Wikipedia illa, ta hanyar yin gyara ko fassara walau mai kyau ko akasi, wanda kan kawo ci baya idan akasi aka samu). Koma tunda an gama gasar ya dace a bi diddigi don taskance su, kasancewa makalolin da aka wallafa anan, na nan don anfanar Al'umma na din-din-din...
- Rashin gyara su illa ce, ya fi kyautuwa mu gyara makalolin da aka riga aka fassara fiye da mu kirkiro sabbi, don kaucewa masu nazari su fahimci abin ba daidai ba wanda hakan illa ce garemu bayan su masu nazarin a wannan kundi. BnHamid (talk) 09:52, 4 ga Yuli, 2024 (UTC)
Eh
gyara sasheEh Akwai gyara ga wasu da ka ƙirƙiro misali WANNAN MAKALAR ta na bukatar gyara kafin a iya fahimtar mi ake nufi. Kuma baza ka haɗa ta da ƴar'uwarta ta Turanci wanda daga nan ka fassaro ta wurin inganci karantawa da Ma'ana ba.
Akwai f'ida makala ta yi gogayya wurin inganci da kusan kashi 80+ bisa 100% daga kishiyarta da aka fassarota daga can duba da fassara ce akayi ba wai sabuwar makala bace. Sannan bin ka'idojin Rubutun Hausa na da amfani. Da fatan zamu gyara. Na gode. BnHamid (talk) 10:03, 4 ga Yuli, 2024 (UTC)
- tom nagode Smshika (talk) 11:14, 4 ga Yuli, 2024 (UTC)
- @BnHamidNagode da tunasarwa, kuma a koda yaushe ina ƙoƙarin ganin na bunƙasa maƙalolin Hausa Wikipedia, ganin Wikipedia encyclopaedia ce wacce ta baiwa kowa damar gyara to inaga idan nayi wata maƙala ba dai-dai ba zaka iya gyarawa batare daka tuntuɓe ni ba, saboda shi ilimi kogi ne ba komai ne zan iya sani ba, sannan kaima idan kayi gyara a wata maƙala dana ƙirƙira ka taimaka wajen bunƙasa ta, nagode. Smshika (talk) 12:59, 4 ga Yuli, 2024 (UTC)
- Eh hakane ta ba ka dama haka-zalika dokar Wikipedia ta yarje a yi gyara musamman gyaran ma kai ne silar sa, kuma nima zan iya gyara ta. Amman cigaba da kirkiro wata ba ka gyara wadda ka ƙirƙiro ba, mike amfanin hakan ? Ko sai gyaran ya kai inda tsirarun mutane ba za su iya da shi ba ?, ko sauri yin wata makalar zai hana ka gyaran wacce ka fara kirkirowa ?, bayan gyaran ya fi amfani fiye da ƙirƙiro wata makalar.
- Ganin kai ka ƙirƙiro ta ya fi kyautuwa ka gyara ta kafin ka yi wata kuma. Hakan zai baka damar kara kwarewa kuma wani editan ma zai kiyaye ki dan ganin an maka gyara akan kuskure rashin hakan kuma zai sa wani ma gobe ya yi. Ɗin haka kin gyara makala kuma ka cigaba da ƙirƙiro wata hakan na nufin wankin hula ya kamu dare. Ya kamata ka kara sani, riga kafi ya fi magani!. BnHamid (talk) 18:05, 4 ga Yuli, 2024 (UTC)
- Kuma da kake cewa ta baka dama. Don haka idan na ga gyara kawai inje in yi ba sai na faɗa maka ba. Ai wannan aikin ba sai ka faɗa ba. Sannan ina so ka sani Nima ita ta bani dama idan ana aikata kuskure inje in gargadi mai yi don magance matsalar daga tushen matsalar kafin ta girmama. Kuma a bisa ka'ida na yi maka gyaran, haka-zalika ba kai kadai aka taba cewa wane ya kamata kayi kaza dalili kaza ba. BnHamid (talk) 18:12, 4 ga Yuli, 2024 (UTC)
- @Smshika. BnHamid (talk) 19:39, 4 ga Yuli, 2024 (UTC)
- To allhmdllh naji duk bayanan ka, abinda zance maka ni dai ina iya bakin ƙoƙari na, inaga ai kai admin ne, to a duk lokacin da kaga wata maƙala wacce nayi wadda bata dace ba ko take da kura-kurai zaka iya goge ta, hakan ma gyara ne kayi wani sai ya sake fassara ta. Nagode Smshika (talk) 19:44, 4 ga Yuli, 2024 (UTC)
- @Smshika ya kamata kasan irin maganar da za ka riƙa yi !. Ka je ka bi tarihin kowa, ba wanda ba'a taɓa yi ma gyara ba a shafin tattaunawar sa. Amman kai an maka magana har zaka buɗa baki kace aje a gyara ba sai an maka magana ba. Wannan maganar kuskure ce da ka fade ta, kasancewar muna mu'amala yadda ya dace a wannan wuri, bugu da kari a dokance na ankarar da kai, sannan abinda ya haɗa mu yafi karfin ka buɗa baki ka faɗi irin waccen maganar.
- Abu na karshe shine na faɗa maka kuma na sauke hakki. So duk wani abu da kai ba ni zai shafa ba, kasancewar akwai dokar ta za tai aiki. BnHamid (talk) 11:41, 5 ga Yuli, 2024 (UTC)
- Masha Allah, nagode sosai da shawara, kuma zan cigaba da iya irin ƙoƙarin da zan iya na bunƙasa Wikipedia, Nagode. Smshika (talk) 14:44, 5 ga Yuli, 2024 (UTC)
- To allhmdllh naji duk bayanan ka, abinda zance maka ni dai ina iya bakin ƙoƙari na, inaga ai kai admin ne, to a duk lokacin da kaga wata maƙala wacce nayi wadda bata dace ba ko take da kura-kurai zaka iya goge ta, hakan ma gyara ne kayi wani sai ya sake fassara ta. Nagode Smshika (talk) 19:44, 4 ga Yuli, 2024 (UTC)
- @Smshika. BnHamid (talk) 19:39, 4 ga Yuli, 2024 (UTC)
- @BnHamidNagode da tunasarwa, kuma a koda yaushe ina ƙoƙarin ganin na bunƙasa maƙalolin Hausa Wikipedia, ganin Wikipedia encyclopaedia ce wacce ta baiwa kowa damar gyara to inaga idan nayi wata maƙala ba dai-dai ba zaka iya gyarawa batare daka tuntuɓe ni ba, saboda shi ilimi kogi ne ba komai ne zan iya sani ba, sannan kaima idan kayi gyara a wata maƙala dana ƙirƙira ka taimaka wajen bunƙasa ta, nagode. Smshika (talk) 12:59, 4 ga Yuli, 2024 (UTC)
Translation request
gyara sasheHello, Smshika.
Can you translate and upload the article about the prominent Turkish economist en:Dani Rodrik in Hausa Wikipedia?
Kindest regards, Moroike (talk) 10:38, 24 Disamba 2024 (UTC)
- HI moroike
- i wiil do it Smshika (talk) 13:16, 24 Disamba 2024 (UTC)
- Thank you. Moroike (talk) 13:48, 24 Disamba 2024 (UTC)
- I've done the translatiom. I really appreciats Smshika (talk) 14:01, 24 Disamba 2024 (UTC)
- Thank you very much for the new article and I wish you a Happy New Year. Moroike (talk) 14:06, 24 Disamba 2024 (UTC)
- Thank you sir Smshika (talk) 14:13, 24 Disamba 2024 (UTC)
- Thank you very much for the new article and I wish you a Happy New Year. Moroike (talk) 14:06, 24 Disamba 2024 (UTC)
- I've done the translatiom. I really appreciats Smshika (talk) 14:01, 24 Disamba 2024 (UTC)
- Thank you. Moroike (talk) 13:48, 24 Disamba 2024 (UTC)