Wikipedia:Shawarwari goma akan gyaran Wikipedia

Zaku iya karanta wannan shawarwarin da Turanci

Shawara ta 1. Kayi rajistar account

gyara sashe

Duk da cewa zaku iya gyaran Wikipedia, tare da rubuta muƙaloli ba tare da kun yi rajistar account ba, yin rajistar yana da matuƙar muhimmanci. Zaku iya zaɓar duk suna ko laƙabin da kuke son amfani da shi, domin yin rijistar kyauta ne. Sannan fahimci cewa duk gyaran da kuka yi, yana akan idanun dukkan editoci da ma masu karatu domin hakan shi ke bada damar sanin abunda kowa ke aiki akai, sannan da gyara abubuwan da ba dai-dai suke ba. Haka zalika, yin rajistar account zai baku wata damar amfani da wasu kebantattun abubuwa wanda sai mai account kawai zai iya amfani dasu, kamar amfani da shafin jerin abubuwan da ake bin sawu.

Shawara ta 2. Ka fahimci manufofi biyar

gyara sashe

Da akwai wasu muhimman manufofin Wikipedia wanda ake kira Manufofi biyar, yana da muhimmanci, ku fahimce su, kuma kuyi ƙoƙarin amfani da su a yayin da kuke gyaran Wikipedia. Yana da kyau, ku fahimci Wikipedia bata kawo rahoton labarai, wato wani abu wanda ba a riga an rubuta shi ba, a wata ingantacciyar hanyar samun bayanai ko kuma a sahihan littattafai. Sannan Wikipedia ba dandalin sada fadar ra'ayi bane inda zaka tallata kanka ko wani naka, kai koma wata hajarka. Wikipedia ta bambanta matuƙa da wasu sauran shafukan sada zumunta, dandalin tattaunawa ko kuma gidajen yanar gizon mujallu da jaridu da kuka saba dasu wanda suke bada damar kowa ya fadi ra'ayinsa yadda yake so. Ita Wikipedia, babbar manufar ta shi ne, tattaro dukkan tabbatacce da kuma sahihin ilimi da bayanan abun da ɗan Adam ya sani zuwa wuri guda domin amfanin kowa da kowa. Kasancewar Wikipedia nada editoci mabanbanta ra'ayoyi daga ko ina a duniya, ya zama wajibi kuyi mu'amala da kowa cikin girmamawa da kwanciyar hankali ko da a lokacin muhawara. Sannan Wikipedia bata da kayyadajjen lokacin da aka dibar mata domin gama rubuta ta, hasalima ita aiki ne wanda baida karshe. Saboda haka a ko da yaushe ana maraba da kai.

Shawara ta 3. Kar ka ji tsoro, amma kasan abun da kake

gyara sashe

Indai kaga wata muƙala dake buƙatar wani gyara, ko yaya ƙanƙantar shi to kar ka ji tsoro, kawai ka aiwatar da gyaran. Wikipedia da ma wasu shafukan yanar gizo ce, ci gaban su yana ta'allaƙa ne ga jajircewar masu bada gudummuwa na sakai. Amma yana da kyau, ku bambance gyara mai ma'ana da kuma gyara mara ma'ana.

Shawara ta 4. Kasan wa kake rubuta mawa

gyara sashe

A lokacin da kake rubuta muƙalar Wikipedia, ka fahimci kana yin rubuta ne wanda kowa da kowa zai iya karantawa a duk faɗin duniya. Saboda haka ka yi amfani da sassaukan kalmomi da kuma cikakken bayani domin fahimtar mutane da yawa. Kada ka yi rubutu irin wanda za'a gabatar a gaban taron farfesoshi kada kuma kayi irin wanda za'a gabatar a gaban yan makarantar firamare; saboda haka rubutun ka ya zama tsaka-tsakiya domin sauƙin fahimta.

Shawara ta 5. Ka guji satar fasaha

gyara sashe

Kasancewar kusan duk abunda ke akan Wikipedia an bada shi a lasisin gama-gari ta yadda kowa zai iya amfani da abubuwan dake cikinta, to ya zama wajibi a kiyaye, duk kuma abunda za a sama Wikipedia shima ya zama yana da irin wannan lasisin. Saboda haka, Wikipedia bata ansar ko wane irin rubutu ko hoto wanda bashi da cikakken izini daga mai hakkin mallakar shi. Kada ku kwafo rubutu daga wasu shafukan yanar gizo, ko a litattafai ko jaridu ba tare da izini ba. Duk rubutun da aka tabbatar an kwafo shi daga wani guri ba tare da izini ba ana goge shi da gaggawa a Wikipedia tare dayin gargaɗi ga mai aikata hakan. Wikipedia ta ɗauki Haƙƙin Mallaka da matuƙar muhimmanci kuma ya zama tilas akan kowane editan Wikipedia ya kiyaye wannan.

Shawara ta 6. Tabbatar da asalin abun da kake rubutawa

gyara sashe

Wikipedia kundin ilimi ne na haƙiƙa. Domin tabbatar da hakan, ya zama tilas duk bayanin da ka bayar ka bada tushensa, wato sahihin wurin kamar jaridu, mujjallu ko litattafai. Haka zalika zaku iya bada tushen bayani ta hanyar malikin su a inda suke akan yanar gizo. Sannan ku fahimci cewa duk bayanin da kuka bayar da tushensa, kowa zai iya bincikawa domin ya tabbatar da gaskiyar al'amarin. Abubuwan da aka gano ba gaskiya bane dole a cire su daga Wikipedia baki ɗaya.

Shawara ta 7. Ka guji tallata kanka ko hajarka

gyara sashe

Talla, kowace kala ce ta yi hannun riga da manufar Wikipedia; ku guje ta. Kada kuyi ƙoƙarin amfani da Wikipedia wajen tallata kanku, ko wani mutum da kuke ƙauna ko kuma wani kasuwanci, ko fahimta ta addini ko siyasa.

Shawara ta 8. Yi amfani da iliminka cikin hikima

gyara sashe

Yana da kyau ku bada gudummuwa a fannin da kuka karanta ko kuka fi sani, kamar ɓangaren ilimin kimiyya, tarihi ko kuma fasahar sadarwa. Amma ku fahimci Wikipedia bata amsar sabon ilimi daka gano ko kuma wani bincike da ka yi, wanda ba a riga an wallafa shi ba a sahiha.

Shawara ta 9. Yi rubutu daga mahangar da ba son rai

gyara sashe

Dukkan muƙaloli dake a cikin Wikipedia ya zama tilas a rubuta su daga mahangar adalci, mahangar da ba bu son rai. In kana rubuta muƙala, ka rubuta iya sahihan bayanai da aka riga aka rubuta a ingantattun litattafai ko sahihan jaridu da makamantansu.

Shawara ta 10. Yi tambaya akan duk abun da baka gane ba

gyara sashe

Wikipedia wani lokaci ta kan yi wahalar fahimta wurin sababbin editoci, musammam ta hanyar amfani wasu da ke wajen sarrafa shafi. Kada ku yi ƙasa a gwuiwa wajen tambaya akan duk wani abu da ya shige maku duhu ko kuke neman ƙarin bayani. Zaku iya neman taimako ta hanyoyi da dama. Ɗaya daga cikinsu shi ne ta hanyar rubuta {{a taimaka mani}} akan shafinku na tattaunawa tare da yin bayani irin taimakon da kuke so. Da zarar kun yi hakan, za a samu wani editan da zai zo ya amsa dukkan tambayoyinku.

*Manufofi Biyar *Shawarwari akan gyaran Wikipedia *Yadda ake rubuta muƙala *Rubutu a mahangar da ba son rai *Ingancin tushen bayanai