Em-mustapha
"Ba zaka taɓa yin nadamar kyautatawa ba!"
Maraba da zuwa shafi na,
Ni ma'aikacin sakai ne a Wikipedia daga jihar Kadunan, Najeriya. Ina taimakawa a wurare daban-daban na manhajojin Wikimedia, daga ciki, akwai wannan manhaja ta Hausa Wikipedia, inda nake da iko na Administrator. Burina a rayuwa shine in kawo sauyi, in canja tunanin mutane zuwa alkhairi da nagarta, na tabbata mutum ɗaya kan iya kawo sauyi a ko'ina, mutuƙar ya jajirce! Lallai hanya mafi sauƙi da zaka taimaki mutum shine ka ilmantar da shi. A nawa ƙoƙarin, shine in taimaka wurin samar da ilimi a Wikipedia, wannan hanya ce ta farko da za'a iya ilmantar da al'ummar duniya baki ɗaya, musamman ga mutanen da yanayin da suka tsinci kansu ya sanya basa iya samun karatu.
Domin ƙarin bayani game da ni, duba;