Sussuka
Sussuka sana'a ce wadda akeyi a ƙauyuka ko kuma muce a zamanin da, wanda yanzu an samu cigaba na tekanoloji da ya kawo injina masu yin wannan aiki na sussuka. Sussuka da casa, duk kusan abu ɗaya ne, sai dai ita sussuka zangarniya hatsi ake bugu, ita kuma casa misali kamar casa wake, masara da dai makamantansu. Menene sussuka kuma suwaye keyinta dame ake yinta? Sune muhimman abubuwa uku da zamu tattauna akai.
Sussuka | |
---|---|
agronomic practice (en) | |
Bayanai | |
Ƙaramin ɓangare na | agricultural activity (en) |
By-product (en) | chaff (en) |
Gudanarwan | barny (en) |
Uses (en) | flail (en) , threshing machine (en) da combine harvester (en) |
Sussuka na nufin cire ƙwayar hatsi ko kuma amfanin gona daga cikin ɓawon shi ko kuma zangarniya ta hanyar amfani da turmi da taɓarya yayi bugu ko kuma casawa, misali sussuka gero, dawa, masara da sauran su. Mafi akasari mata ne akafi sani da sana'a sussuka, wato (sussukau) musamman tsofaffi, duk da kuma cewa wani lokacin maza suma sunayin sussuka amma ba kamar yadda mata keyi da turmi da taɓarya su maza suna samun kulki ne wato sanda mai kauri sai abaza zangarniya hatsi a falali ko a kan wata Shimfiɗa wadda aka tanada don yin sussuka/Bugu. [1] Anayin sussuka ne da turmi da taɓarya Sannan kuma akan ware filin ne a can gefen gari don yin sussuka da bugun dawa ko gero ko kuma bayan gida a zamanin da. Ana kiran wajen da ake sussuka da (masussuki/masussuka) kamar yadda ya gabata ana amfani da turmi da taɓarya, sai kwarya da faifai don shiƙa hatsi da kuma rairaya yayin da aka gama sussuka, ita shiƙa anayinta bayan an kammala sussuka don fitar da hatsi daga wannan ƙaiƙayin nashi ko kuma kwalfa, Ko kwasa.
Manazarta
gyara sashe- ↑ "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2021-04-18. Retrieved 2021-04-29.