Sunday Fajinmi
Sunday Olawale Fajinmi ɗan siyasar Najeriya ne kuma ɗan kasuwa.
Sunday Fajinmi | |||
---|---|---|---|
Mayu 1999 - Mayu 2003 - Akinlabi Olasunkanmi → District: Osun West | |||
Rayuwa | |||
Haihuwa | jahar Osun, Nuwamba, 1952 (72 shekaru) | ||
ƙasa | Najeriya | ||
Harshen uwa | Yarbanci | ||
Karatu | |||
Harsuna |
Turanci Yarbanci | ||
Sana'a | |||
Sana'a | ɗan siyasa | ||
Imani | |||
Jam'iyar siyasa | Alliance for Democracy (en) | ||
senatorsundayfajinmi.com |
Ilimi
gyara sasheFajinmi ya kammala karatunsa na gaba a jami'ar Teesside kuma ya ci gaba da ba da hidimar ƙasa a matsayin memba na National Youth Service Corps (NYSC) a loƙacin da yake aiki a Nigerian Airways .
Sana'a
gyara sasheAn zaɓi Fajinmi Sanata mai wakiltar mazaɓar Osun ta Yamma a jihar Osun a Najeriya a farkon jamhuriya ta hudu ta Najeriya, inda ya tsaya takara a karkashin jam'iyyar Alliance for Democracy (AD). Ya fara aiki a ranar 29 ga Mayu 1999.
Sana'ar siyasa
gyara sasheAn zaɓi Sanata Sunday Olawale Fajinmi a matsayin Sanata a shekarar 1998 mai wakiltar mazaɓar Osun ta yamma a ƙarƙashin jam'iyyar United Nigeria Congress Party (UNCP) a loƙacin mulkin Janar Sani Abacha na mulkin soja. Bayan an dawo da mulkin dimokuraɗiyya, a watan Yunin 1999 aka sake zaɓensa a matsayin Sanata, Osun ta yamma a kan dandalin kawancen dimokradiyya inda ya doke Isiaka Adetunji Adeleke na jam’iyyar People’s Democratic Party.
Yayin da yake majalisar dattijai, an naɗa shi a kwamitocin Kimiyya & Fasaha, Sufuri, Jiha & Kananan Hukumomi (Mataimakin Shugaban Ƙasa), Watsa Labarai, Harkokin Gwamnati da Harkokin Tattalin Arziki. A watan Disambar 2005 ya koma jam'iyyar PDP mai mulki.
Fajinmi ya kasance dan takarar gwamna na jam’iyyar Alliance for Democracy a zaɓen jihar Osun da aka gudanar ranar 9 ga watan Agustan 2014.