Shuaibu Audu
An taskan ce wannan muƙalar a cikin jerin Muƙaloli_masu_kyau a Hausa Wikipedia
Ana sa ran wata rana wannan muƙalar zata kasance a Babban Shafin Muƙalar mu a yau |
Shuaibu Abubakar Audu (an haife shi ranar 6 ga Nuwamba 1980) ma'aikacin banki ne kuma ɗan siyasa a Najeriya.[1][2] Shine ministan cigaban ƙarafa a yanzu tun daga watan Agustan 2023.[3]
Shuaibu Audu | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | 6 Nuwamba, 1980 (44 shekaru) |
Sana'a | |
Sana'a | ɗan siyasa da investment banker (en) |
Kafin a naɗa shi minista, ya kasance ɗan takarar gwamna a Jihar Kogi.[4] Bayan gabatarwa da tantance sunayen ministocin da majalisar dattawa ta yi, an naɗa Audu a matsayin ministan bunƙasa ƙarafa a ranar 16 ga watan Agusta, 2023.[5]
Rayuwar farko da ilimi
gyara sasheAn haifi Audu ga Abubakar Audu a Kogi.[6] Ya halarci Jami'ar Leicester da ke Burtaniya inda ya sami digiri na farko a fannin tattalin arziki da kasuwanci a shekarar 2001. Ya sami digiri na biyu a Makarantar Kasuwancin Henley, University of Reading.[7] Audu ya samu digirin digirgir a fannin kasuwanci (MBA) a jami'ar Oxford a shekarar 2013[8] inda ya kasance memba na St Hugh's College.[9]
Sana'a
gyara sasheStanbic IBTC (2013 - 2023)
gyara sasheShuaibu Audu ya yi aiki a Legas a matsayin manazarcin zuba jari tare da kamfanin Stanbic IBTC. Ya kuma taba zama babban darakta na reshen kula da kadarorin bankin.[10]
Audu ya yi aiki a matsayin babban jami’in gudanarwa na Stanbic IBTC Investment, na tsawon shekaru 10 har zuwa lokacin da ya shiga harkokin siyasa gadan-gadan.[11][12]
Siyasa (2023)
gyara sasheAudu dai ɗan jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ne inda ya tsaya takara a matsayin ɗan takarar gwamna na jam’iyyar a reshen Jihar Kogi.[11]
A watan Fabrairun 2023, ya bayyana aniyarsa ta takara[13] a zaɓen gwamnan jihar Kogi a watan Nuwamban 2023 a ƙarƙashin jam’iyyar All Progressives Congress (APC).[14]
Ya rasa tikitin takarar gwamna a hannun Ahmed Ododo a zaɓen fidda gwani na watan Afrilu 2023.[15][16][17][18]
A watan Agustan 2023, Shugaba Bola Tinubu ya naɗa shi Ministan Raya Karfe.[19][20]
Rayuwa ta sirri
gyara sasheShuaibu Audu ɗan tsohon gwamnan jihar Kogi, Abubakar Audu ne. Yana da aure da ƴaƴa.[8]
Manazarta
gyara sashe- ↑ Obahopo, Boluwaji (6 July 2021). "Kogi 2023 Guber Race: Shuaibu Audu most qualified to govern Kogi ― Group". Vanguard Nigeria. Retrieved 20 August 2023.
- ↑ Lokoja, Muhammad Bashir; Telegraph, New (2021-07-05). "Kogi 2023: Shuaibu Audu's capable of fixing Kogi – Group". New Telegraph (in Turanci). Retrieved 2023-08-20.
- ↑ Pai, Bilkisu Halilu (2023-08-16). "President Tinubu Assigns Portfolios To Ministers Designate". Voice of Nigeria (in Turanci). Retrieved 2023-08-20.
- ↑ Amodu, Taiwo (2023-04-15). "Kogi APC Primary: Smart Adeyemi, Audu, Oseni, others reject outcome". Tribune Online (in Turanci). Retrieved 2023-08-20.
- ↑ Ogundapo, Abdulqudus (2023-08-04). "Profiles of President Tinubu's 19 fresh ministerial nominees". Premium Times Nigeria (in Turanci). Retrieved 2023-08-20.
- ↑ "In Praise of Shuaibu Audu - THISDAYLIVE". www.thisdaylive.com (in Turanci). Retrieved 2023-08-20.
- ↑ Partners, N. M. (2023-08-21). "Meet Oxford- trained Shuaibu Abubakar Audu, investment expert to man Nigeria's Ministry of Steel Development". Nairametrics (in Turanci). Retrieved 2023-08-24.
- ↑ 8.0 8.1 Taoheed, Adegbite (2023-03-09). "INTERVIEW: I want to govern Kogi to reclaim our land, restore our values — Prince Shuaib Abubakar Audu". Tribune Online (in Turanci). Retrieved 2023-08-20.
- ↑ Ogundapo, Abdulqudus (2023-08-04). "Profiles of President Tinubu's 19 fresh ministerial nominees". Premium Times Nigeria (in Turanci). Retrieved 2023-08-23.
- ↑ Onuh, Chioma (2023-08-07). "Equity, fairness informed nomination of Shaibu Audu - Bello". Businessday NG (in Turanci). Retrieved 2023-08-20.
- ↑ 11.0 11.1 "Kogi Guber: 18 APC Aspirants Square Up To Succeed Bello - THISDAYLIVE". www.thisdaylive.com (in Turanci). Retrieved 2023-08-20.
- ↑ Ogacheko, Idoko Daniel (April 4, 2023). "Time to reward sacrifices of late Prince Abubakar Audu is now". The Nation Online. Retrieved August 21, 2023.
- ↑ Omidiji, Rachael (2023-02-23). "Prince Shuaib Abubakar Audu unveils His seven point agenda for Kogi State development". Tribune Online (in Turanci). Retrieved 2023-08-20.
- ↑ Agba, George (2023-02-23). "Abubakar Audu's Son Joins Kogi Guber Race, Picks Forms" (in Turanci). Retrieved 2023-08-20.
- ↑ Akinfehinwa, John (2023-04-17). "Kogi APC guber primary, biggest fraud in Nigeria's political history - Shuaibu Audu". Daily Post Nigeria (in Turanci). Retrieved 2023-08-20.
- ↑ Ijaseun, David (2023-05-06). "Audu withdraws suit against APC guber candidate in Kogi". Businessday NG (in Turanci). Retrieved 2023-08-20.
- ↑ Report, Agency (2023-07-18). "Again, court affirms Ododo as Kogi APC governorship candidate". Premium Times Nigeria (in Turanci). Retrieved 2023-08-20.
- ↑ Report, Agency (2023-04-18). "Audu's son faults Kogi APC gov primary, threatens lawsuit". Punch Newspapers (in Turanci). Retrieved 2023-08-20.
- ↑ Emmanson, Jerry (2023-08-05). "Rivers East Senator Hails Kogi Ministerial Nominee, Shaibu Audu, Over Credentials, Honesty" (in Turanci). Retrieved 2023-08-20.
- ↑ TVCN (2023-08-16). "President Tinubu To Swear In Ministers On Monday August 21 - Nigeria News" (in Turanci). Retrieved 2023-08-20.