Sagir Adamu Abbas farfesa ne, malami ne, mai gudanarwa, sannan kuma mataimakin shugaban Jami'ar Bayero Kano na 11.[1]

Sagir Adamu Abbas
Rayuwa
Haihuwa jihar Kano, 22 ga Afirilu, 1962 (62 shekaru)
ƙasa Najeriya
Karatu
Makaranta Jami'ar Bayero
University of Bristol (en) Fassara
Harsuna Turanci
Hausa
Pidgin na Najeriya
Sana'a
Sana'a Malami da malamin jami'a
Employers Jami'ar Bayero
Imani
Addini Musulunci

Tarihinsa

gyara sashe

An haifi Sagir ne a ranar 22 ga Watan Afrilun shekarar ta 1962 a Yan Katifa, Kofar Madabo mazauna karamar Hukumar Kano, Jihar Kano.

Abbas ya fara aiki ne a matsayin malami a Sashin Lissafi a Kwalejin Ilimi ta Sa’adatu Rimi da ke Kumbotso. Ya shiga Jami’ar Bayero Kano a matsayin Mataimakin Malami a shekarar ta 1991, ya kuma rike mukamai daban-daban da suka hada da Shugaban Sashen Ilimi, da Shugaban riko na tsangayar ilimi.

An nada Abbas Darakta a ofishin raya kasa, daga shekarar ta 2004 zuwa 2007. Daga watan Afrilu 2010 zuwa Satumba 2013, ya kasance babban mataimaki na musamman ga tsohuwar ministar ilimi, Farfesa Ruqayyah Ahmed Rufa’i. Ya kuma rike mukamin Darakta na Hukumar Bincike, Sabuntawa, da Haɗin gwiwar. A ranar 26 ga Maris, 2015, Majalisar gudanarwa ta Jami’ar Bayero Kano ta nada Abbas a matsayin mataimakin shugaban jami’a (Academic), wanda ya gaji Farfesa Hafiz Abubakar.[2]

A shekarar ta 2020 Abbas ya zama mataimakin shugaban jami’ar Bayero Kano na 11.[3][4][5]

Nasara a matsayin shugaban jami'a

gyara sashe

Karkashin jagorancin Sagir Abbas shugaban jami’ar Bayero Kano na 11 ya samu nasarori da dama tare da samun lambobin yabo daban-daban, wanda hakan ya kara daukaka darajarta a duniya. A lokacin aikinsa, jami'ar ta kuma aiwatar da wani shiri na daukar dalibai aiki na wucin gadi a cikin jama'ar harabar. Waɗannan ayyuka sun haɗa da sa ido kan wuraren makaranta da tsaftace muhalli, tare da ɗalibai suna karɓar diyya kowane wata don ƙoƙarinsu.[6]

A lokacin da yake rike da mukamin shugaban jami’ar Bayero Kano ta kasance a cikin manyan jami’o’i a yankin kudu da hamadar Sahara.[7]

A ranar 22 ga watan Yuli, yayin taron kungiyar jami’o’i karo na 56, shugaban jami’ar Sagir Abbas ya sanar da cewa an ware miliyoyin nairori a matsayin matakan shawo kan matsalar kudi sakamakon karin farashin man fetur da kuma kudaden rajista. Ya kuma tabbatar da cewa za a samu lamuni marar riba ga ma’aikatan.[8]

Manazarta

gyara sashe
  1. "Council Appoints Prof Sagir Abbas as 11th Vice Chancellor of BUK | Bayero University, Kano". www.buk.edu.ng. Archived from the original on 28 October 2020. Retrieved 2021-02-09.
  2. "Council Confirms Prof. Sagir Abbas, DVC Academics | Bayero University, Kano". buk.edu.ng. Retrieved 2021-02-09.
  3. "Professor Abbas takes over as BUK VC". Daily Trust (in Turanci). Archived from the original on 14 February 2021. Retrieved 2021-02-09.
  4. University, Skyline. "SUN Management Team Pays Courtesy Visit to Bayero University Kano (BUK) in Honour of New Vice-Chancellor". www.sun.edu.ng (in Turanci). Archived from the original on 26 September 2020. Retrieved 2021-02-09.
  5. https://www.nuc.edu.ng/adamu-adamu-commissions-buks-abubakar-rasheed-senate-building/creati [dead link]
  6. "Sagir Adamu Abbas Archives". Peoples Gazette (in Turanci). Archived from the original on 6 July 2024. Retrieved 2023-07-14.
  7. "BUK Rankings | Bayero University". www.buk.edu.ng. Archived from the original on 23 July 2023. Retrieved 2023-07-23.
  8. kabir (2023-07-22). "Fuel Price Hike: BUK Rolls Out Palliatives for Staff, Students". PRNigeria News (in Turanci). Archived from the original on 23 July 2023. Retrieved 2023-07-23.