Rijiyar Nagwamatse wurin yawon shakatawa ne d kuma tarihi na tsawon shekaru 150, da ke da nisan kilomita 20 zuwa Kontogora, Najeriya.[1]

Rijiyar Nagwamatse
General information
Labarin ƙasa
Map
Tsarin Daidaiton Labarin Kasa 10°24′N 5°28′E / 10.4°N 5.47°E / 10.4; 5.47
Kasa Najeriya

Tarihin Rijiyar

gyara sashe

Ana zuwa wajen rijiyar don yawon buɗe ido tana ɗauke da ruwan da aka fara tonowa daga wajen wanda ya kafa Masarautar Kontogora ta gargajiya Umaru Nagwamatse, inda rijiyar ke kwance a daidai wurin Nagwamatse ya yi wani abin al'ajabi ta hanyar amfani da yatsansa na dama ya tona sannan ruwa ya fito daga ƙasa. daga al’ummar masarautar sun ce ya kan yi Alwala don sallar la’asar. Kamar yadda mazauna masarautar ta Sudan suka shaida wa jaridar Aminiya cewa ruwan bai taɓa ƙafewa ƙasa da ƙada shida.

A rahoton da jaridar Independent Newspaper fitar cewa lokacin da Nagwamatse yake fita Jihad zuwa Najeriya ta tsakiya yana hutawa a ƙarƙashin bishiya, yana kan hutawa sai lokacin sallah yayi kuma ba ruwa kusa kawai sai ya kafa takobin sa a gun sannan ya tona da hannunsa sai ruwa ya ɓullo to har yanzu rijiyar tana nan. Nagwamatse shi ne ɗan Sarkin Musulmi na biyar kuma shi ne yankin da aka kafa Masarautar Sarkin Sudan Kontogora tare da ƴa'ƴansa biyu Ibrahim Nagwanatse da Abubakar Modibo, jarumi ne kuma yariman masarautar sakkwato wanda ya zo don yayi mulki daga guri mai nisa. Masarautar iyayensa da suka kafa masarautun da aka fi sani da Kontogora ta Jihar Neja a wani rahoto daga Abdullahi Musa ya ce lokacin da ya isa Masarautar ne da tsakar rana ta shekarar 1864. Kuma a yau wannan rijiyar tazama wurin yawon buɗe ido kuma sanannen wurin ziyara a Arewa, Yankin Najeriya.[2][3][4]

Manazarta

gyara sashe
  1. "Where to visit in Niger state". Independent Newspaper. Retrieved 23 April 2020.
  2. Abubakar, Uthman; Kontagora, who was in (2009-10-18). "150-Year Heritage of a Prince of Sokoto Caliphate". Daily Trust (in Turanci). Retrieved 2020-04-23.[permanent dead link]
  3. "Nagwamatse Well". ZODML (in Turanci). Retrieved 2020-04-23.[permanent dead link]
  4. Ibenegbu, George (2017-11-03). "Top 10 facts about the ☛biggest state in Nigeria by area". Legit.ng - Nigeria news. (in Turanci). Retrieved 2020-04-23.[permanent dead link]