Remi Aduke Adedeji (an haifeta a shekarar 1937) marubuciyar littafin Yara ce a Najeriya.

Remi Adedeji
Rayuwa
Haihuwa Okemesi (en) Fassara, ga Afirilu, 1937 (87 shekaru)
ƙasa Najeriya
Harshen uwa Yarbanci
Karatu
Harsuna Turanci
Yarbanci
Pidgin na Najeriya
Sana'a
Sana'a Marubiyar yara, edita da marubuci
Muhimman ayyuka Moonlight Stories (en) Fassara

Tarihin Rayuwa

gyara sashe

An haifi Adedeji a Okemesi a jihar Ekiti a shekarar 1937.[1] Adedeji ta ji takaicin littattafan Yara da ba su nuna al'adun Afirka ba. Yawancin labaranta sun samo asali ne daga tatsuniyoyi na Najeriya. [1] Ta rubuta gami da buga littafin The fat woman (Mata mai ƙiba) a shekarar 1973.[2] Ta zama editan ga mujallar ilimi, Bookbird.[3] Littattafanta akai-akai sun ƙunshi dabi'un kunkuru (dabba kunkuru). Littafinta na (Moonlight Storie)-"Labarun Hasken Wata" na 1986 ya ƙunshi labarai da dama da suka bayyana dalilin da yasa ungulu ke da gashi ko kuma dalilin da yasa ƙoƙon kunkuru ya bayyana.[4]

  • Mace mai ƙiba (The fat woman), 1973.
  • Baba Ojo da Iyalansa (Papa Ojo and his family), 1973.
  • Likacin labarai (It is time for stories), 1973.
  • Labarai kwara hudu game da kunkuru (Four stories about the tortoise), 1973.
  • Labaran da mahaifiyata ta faɗa man ( Stories my mother told me), 1978.
  • Bikin zagayowar ranar haihuwar Tunde (Tunde's birthday party), 1983.
  • Tunde ya ziyarci birnin Ibadan (Tunde visits Ibadan), 1983.
  • Tunde Karon farko a makaranta (Tunde's first day at school), 1983.
  • Moonlight stories: how the tortoise married the king's daughter and other stories, 1986.[4]
  • Dear uncle, 1986.[2]

Manazarta

gyara sashe
  1. 1.0 1.1 Remi Adedeji, Ohio University, Retrieved 27 February 2016
  2. 2.0 2.1 Remi Adedeji, A Bibliography of Anglophone Women Writers, Tony Simoes da Silva, aflit.arts.uwa.edu.au, Retrieved 27 February 2016
  3. Adedeji, Remi (1999). Moonlight Stories (in Turanci). Heinemann Educational Books. ISBN 978-978-129-248-4.
  4. 4.0 4.1 Moonlight Stories, African Book Collective, Retrieved 27 February 2016