Philips Tanimu Aduda

Dan siyasar Najeriya

Philips Tanimu Aduda ɗan siyasan Najeriya ne. Yaci takarar Majalisar Wakilai a Nigeria har karo Biyu, tsakanin shekara ta 2003 zuwa shekara ta 2011,A ranar 9 ga watan afrelu yaci zaben takarar majalisar dattawan a Abuja,[1] Wanda ya tsaya a Dan takarar jam'iyyar PDP.People Demucracy Party . [2][3][4]

Philips Tanimu Aduda
mamba a majalisar dattijai ta Najeriya

11 ga Yuni, 2019 -
District: FCT Senatorial District
mamba a majalisar dattijai ta Najeriya

9 ga Yuni, 2015 - 9 ga Yuni, 2019
District: FCT Senatorial District
mamba a majalisar dattijai ta Najeriya

6 ga Yuni, 2011 - 6 ga Yuni, 2015
District: FCT Senatorial District
mamba a majalisar wakilai ta Najeriya,

5 ga Yuni, 2007 - 6 ga Yuni, 2011
District: Municipal/Bwari
mamba a majalisar wakilai ta Najeriya,

3 ga Yuni, 2003 - 5 ga Yuni, 2007
District: Municipal/Bwari
Rayuwa
Cikakken suna Philips Tanimu Aduda
Haihuwa Abuja, 1953 (70/71 shekaru)
ƙasa Najeriya
Karatu
Makaranta Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Kaduna
Jami'ar, Jos
Harsuna Turanci
Pidgin na Najeriya
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa
Imani
Jam'iyar siyasa Peoples Democratic Party

Farkon rayuwa da Karatu

gyara sashe

An haifi Aduda a garin Karu,FCT Abuja. Yayi karatu a makarantar Sakandiren Gwamnati, sake Gwagwalada (1983–1987) da Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Kaduna (1987 - 1991) don karatun sakandare. Yayi Karatu a Jami’ar Jos (1990–1992) Wanda ya sami shahadar kammala karatu ta difloma a ayyukan zamantakewar al’umma da ci gaban al’umma.Ya kasance Manajan kamfanin Aduda Nigeria Limited daga shekara ta1992 zuwa shekara ta 1995. A kuma Federal Polytechnic,Bida,reshen Abuja (1993–1997) ya sami takardan kammala karatu ta babbar difloma a harkar mulki.Wanda kuma dan uwansa,Gabriel Aduda shi ne Babban Sakatare Tarayya.Yayi dukkan zaben sa a jam'iyar Pdp ne,yanzu haka sanata ne mai wakiltar Abuja.

Harkar siyasa

gyara sashe

A shekarar ta 1996, Aduda ya yi takara a matsayin Kansilan yankin Karu kuma yaci zaben, a Abuja, kuma ya rike mukamai daban-daban a Majalisar Karamar Hukumar Abuja. An zabe shi a matsayin dan majalisar wakilai ta AMAC / Bwara a Abuja a shekara ta (2003 zuwa 2007), sannan aka nada shi Shugaban kwamitin majalisar a kan Babban Birnin Tarayya (Abuja), kuma shi memba na sauran kwamitocin. An sake zabensa a matsayin dan majalisar wakilci yankin Bwari, a Abuja shekara ta 2008.[5] In October 2009, he was given the Best Performing Legislator Award for his contribution to the development of the people.<ref> A watan Oktoba na shekarar 2009, an ba shi Kyautar lanbar yabo a matsayin dan Majalisan da yafi bawa mutane Gudummawarsa

Kafin zaben a ranar 9 ga watan afirelu shekara ta 2011, kugiyouin da suke cikin garin Abuja suka yanke shawarar marama Aduda baya, akan fitowar shi takarar majalisar dattawa. kuma kwana Biyu kafin zabe, 'yan bindiga suka sace dan takarar jam'iyar Labour Party candidate Kayode Ajulo was abducted by gunmen. In the elections, Aduda won 105,562 votes. His main remaining opponent, Musa Tanko Abari of the Congress for Progressive Change (CPC), scored 54,307. After his swearing in, he was appointed Chairman Senate Committee on Power.

A ranar 28 ga watan Maris, na shekara ta 2015 aka sake zabarsa zuwa Majalisar Dattawan Najeriya a karo na biyu yana wakiltar Babban Birnin Tarayya (Abuja) Bayan sake tsayawa takara, abokin hamayyarsa Sani Sidi ya maka Aduda kara a kotun sauraren kararrakin zabe bisa dalilan magudin zaben amma aka yi watsi da karar kuma aka sanar da Adudua a matsayin halastaccen wanda ya lashe zaben. A cikin shekara ta 2017, an nada shi a masayin Mai Tsawatarwa na Majalisar Dattawa.

A ranar 26 ga watan Fabrairun shekara ta 2019, an sake zabarsa a karo na uku a majalisar dattawan Najeriya . Aduda ya yi nasarar lashe zaben da jimillar kuri'u 263,055.

  1. Sunday, Ochogwu (2021-10-21). "FCT Minister condoles Sen Aduda on father's death". Daily Post Nigeria (in Turanci). Retrieved 2022-03-17.
  2. Cite error: Invalid <ref> tag; no text was provided for refs named Mirror20110411
  3. "Senate committee on power wants improved power supply". aitonline.tv (in Turanci). Retrieved 2019-05-01.
  4. "Sanatoci sun ki amincewa a bai wa 'yan Nigeria N5,000". BBC News Hausa. Retrieved 2019-05-01.
  5. Cite error: Invalid <ref> tag; no text was provided for refs named self

Manazarta

gyara sashe