Paulin Soumanou Vieyra
Paulin Soumanou Vieyra, (31 Janairu 1925 - 4 Nuwamba 1987) darektan fina-finan Dahomeyan/Senegal ne kuma masanin tarihi. Yayin da ya zauna a ƙasar Senegal bayan ya kai shekaru 10, an fi danganta shi da wannan al'ummar.
Paulin Soumanou Vieyra | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | Porto-Novo, 31 ga Janairu, 1925 |
ƙasa |
Benin Senegal Faransa |
Mutuwa | Faris, 4 Nuwamba, 1987 |
Ƴan uwa | |
Abokiyar zama | Myriam Warner-Vieyra |
Yara |
view
|
Karatu | |
Makaranta | Institut des hautes études cinématographiques (en) |
Harsuna | Faransanci |
Sana'a | |
Sana'a | darakta, filmmaker (en) da mai sukar lamarin finafinai |
IMDb | nm0896895 |
Fage
gyara sasheAn haife shi a Porto Novo, Dahomey, kuma ya yi karatu a ƙasar Paris, Faransa, [1] inda ya yi karatu a Institut des hautes études cinématographiques. A cikin shekarar 1955 a Paris,[2] inda yayi karatu a Institut des hautes études cinématographiques.[3] ya nuna fim ɗin Afirka na farko, Afrique-sur-Seine. Sauran muhimman nasarorin da ya samu na fim a Afirka sun haɗa da kafa Fédération Panafricaine des Cinéastes a 1969. Ya yi aiki a matsayin darekta na Actualités Sénégalaises, muhimmin sabis na labarai a cikin shekaru ashirin bayan samun yancin kai na Senegal.[4]
A shekara ta 1971, ya kasance mamba na juri a 7th Moscow International Film Festival.[5] Bayan shekaru biyu, ya kasance mamba na juri a 8th Moscow International Film Festival. A shekarar 1985 ya kasance memba na juri a 14th Moscow International Film Festival.[6]
Ya mutu a Ƙasar Paris a shekarar 1987, yana da shekaru 62. [7]
Rayuwa ta sirri
gyara sasheA cikin shekarar 1961, ya auri mawakiya Myriam Warner na Guadeloupe. Ɗaya daga cikin 'yan uwansa Justine Vieyra, haifaffen Parakou.
Ayyuka
gyara sasheFina-finai
gyara sashe- 1954 : C'était il y a quatre ans
- 1955 : Afrique-sur-Seine
- 1957 : L'Afrique à Moscou
- 1958 : Le Niger aujourd’hui
- 1959 : Les présidents Senghor et Modibo Keita ; Avec les Africaines à Vienne ; Présence Africaine à Rome
- 1960 : Indépendance du Cameroun, Togo, Congo, Madagascar
- 1961 : Une nation est née
- 1963 : Lamb ; Voyage du président Senghor en Italie ; Voyage présidentiel en URSS
- 1964 : Avec l’ensemble national ; Écrit du Caire ; Sindiely ; Voyage du président Senghor au Brésil
- 1965 : N'Diongane
- 1966 : Le Sénégal au festival national des arts nègres ; Môl
- 1967 : Au marché ; La bicyclette ; Le gâteau ; Le rendez-vous
- 1974 : Écrit de Dakar ; L’art plastique
- 1976 : L'Habitat rural au Sénégal ; L’Habitat urbain au Sénégal
- 1981 : Birago Diop ; En résidence surveillée, L’envers du décor ; Les oiseaux
- 1982 : Iba N'diaye
Littattafai
gyara sashe- Le Cinéma et l'Afrique, 1969
- Sembène Ousmane cineaste, 1972
- Le Cinéma africain des origines a 1973, 1975
- Le Cinéma au Sénégal, 1983
Manazarta
gyara sashe- ↑ Houngnikpo & Decalo 2013, p. 357.
- ↑ Houngnikpo & Decalo 2013, p. 357.
- ↑ Roy Armes (2008). Dictionary of African Filmmakers. Indiana University Press. p. 129. ISBN 0-253-35116-2.
- ↑ Lena, Marco (Spring 2022). "Paulin Soumanou Vieyra in the Documents of the Rediscovered Audiovisual Archive of the Senegalese Ministry of Culture". Black Camera (in Turanci). 13 (2): 474–488. doi:10.2979/blackcamera.13.2.26. ISSN 1947-4237.
- ↑ "7th Moscow International Film Festival (1971)". MIFF. Archived from the original on 2014-04-03. Retrieved 2012-12-22.
- ↑ "14th Moscow International Film Festival (1985)". MIFF. Archived from the original on 2013-01-16. Retrieved 2013-02-08.
- ↑ "Vieyra, Paulin Soumanou", Library of Congress.