Fina-Finan Hausa
Fina-finan hausa wanda aka fi sani da Hausa fim, shiri ne da Hausawa ke yi don nuna al’adunsu da jawo hankalin al’umma akan rayuwa, musamman na hausawa da al’adunsu[1]. Masana sun nuna cewa fina-finan hausa sun samo asaline daga wasanni na gargajiya wanda akafi sani da wasan kwaikwayo.
Wasan Kwaikwayo.
gyara sasheWannan al’amari ne mai tsohon tarihi matuƙa.Ya samo asali ne daga shekaru aru-aru a daulolin girkawa da rumawa na zamanin da suka shuɗe. Akanyi wasan kwaikwayo ne don nishaɗantar da rundunonin soja da suka ci nasara a yaƙe-yaƙensu na wancen zamani. Sannan akanyi wasan kwaikwayo don farantawa sarakuna rai ta hanyar kiɗe-kiɗe, hikayoyi, raye-raye, da kuma barkwanci. To ta haka wasan kwaikwayo ya wanzu a nahiyoyin duniya[2].
Daga nan harkar wasan kwaikwayo ta bunƙasa ta zama ruwan dare har masu kuɗi kan biya domin a shirya masu wasan kwaikwayo. Nan da nan wasan kwaikwayo ya zama sana’a ta bazu ko ina afaɗin duniya, musamman lokacin da masana’antu suka samu a yammacin turai[3].
A nan ƙasar hausa ana iya cewa wasan kwiakwayo ya daɗe ainun tun hanyoyin yaɗa al’adar gargajiya ta farko. Irin su “Ga Mai Rama ga Daudu”, tatsuniyoyi, da wasan dandali daga bya suka inganya bayan fafa gidagen rediyoyi da tevebijin a kaduna zamanin Ahmadu Bello[4].
Tsakanin shekarar 1963, zuwa 1965, aka fara wasan kwaikwayo mai suna kukan kurciya” wanda ke nuni ga halayne al’umma managarta da kyawawan dabi’un zamantakewar rayuwa[5]. Sabanin ra’ayi al’ada, addini, harshe sun kawo mishkila sosai a farko[6]
Kadan daga cikin jaruman fim na loacin sun hada da, shrib lawal adamu (larp da gpa,) usman Danjuma (kasagi) Sani gwarzo ( tumbuleke) Mansur kwalli, (garuje) da sauransu[7]
Wasu dake jagorancin shirye shiryen wasan kwakwayo na lokacin da daukar nauyi sun hada da Alhaji Yusuf Ladan, Kasimu Yero, Usman Babba Pategi, Alh. Adamu Auge, da Alhaji Bello Abubakar wanda ke taimakawa wajen shirye-shirye kaman “uli ya menta b sabo, Golobo, saun jali, idan matambayi, tumbin giwa, ga fili ga mai doki, Zaman Duniya, da sauransu. – 7 oct, 1982[8].
Bayan jamuriya ta biyu inda aka samu karin kafafen sadarwa an sami ci gaba sosai a harkar wasan kwaikwayo a Nijeriya, musamman da samuwar marubuta, da yawaitar kamera bidiyo da wayewar matasa da bunkasar ilimin zamani.[9]
Fitattun ƴan wasan kwaikwayo na Hausa fim.
gyara sasheMata | Maza |
Aisha musa | Ibrahim mandawari |
Hajiya amina (uwa maba da mama) | Hamisu lamido (iyan tama) |
Hajara usman (hajjo) | Rabilu Musa (Ibro) |
Hafsatu Sharada (Mai Aya) | Ali Nuhu (king of kannyood) |
Hauwa’u Ali Dodo ( Biba problem) | Bashir Bala (ciroki) |
Jamila Haruna | Nura husaini (damo sarkin hakuri) |
Fati Muhammad ( Zubaina) | Kabiru na kwango |
Abida Muhammad | Shehu hassan kano |
Hussaina Gombe (tsigai) | Zulkifl Muhammad (zic) |
Salma Muhammad (Yarinya mai Tsada) | Ishaq sidi ishaq (yaro dan kwalisa) |
Halima Adamu Yahya | Mustapha muhammad |
Hadiza kabara | Shu’aibu lawan (Kumurchi) |
Ruqayya Dawayya (A koyi sana’a) | Alasan inalle |
Ainau Ade | Sani Musa Danja (Danja) |
Hasiya (Aaya) | Umar Yahaya Mahuta |
Rabi So (huma) | Isha Bello (dattijon kirki) |
Hadiza Aliyu (Gabon) | Falalu A Dorayi |
Saratu Gidado (daso) | Adam A Zango (prince) |
Matsaloli.
gyara sashe1. Rashin jari.
2. Rashin fahimtar masu hannu da shuni ga muhimmancin zuba jari da kafa kanfanoni don haɓaka sana’ar fim.
3. Dokoki masu tsauri na ƙasa.
4. Talauci da ya hana cikakken aiki.
5. Kwaikwayon wasu al’adu da suka saɓa ɗabi’un hausawa.
6. Ƙyama ga masu harkar musamman ga wanda basu fahimci muhimmancin harkar ba.
7. Tsoro a zukatan wasu iyaye na mummunan fahimta da za’a riƙa wa ‘ya’yan su[10].
Shawarwari.
gyara sashe1. Samar da kyakkyawan yanayi ta hanyar doka da zata halasta kuma ta haɓaka harkan.
2. Ƙara wayar wa mutane kai kan harkar fina finan hausa.
3. Tabbatar da ingancin fitar da kyawawan ɗabi’u da al’adu na bahaushe a harkar.
4. Kaucewa batsa, ɓatanci, baɗala da duk wata mummunan ɗabi’a.
5. Ƙara fito da sutura, kamala, sana’a da balagar bahaushe a cikin shirye- shiryen wasan kwaikwayo[9].
Bibiliyo.
gyara sasheHausa home videos : technology, economy and society. Adamu, Abdalla Uba, 1956-, Adamu, Yusuf Muhammad., Jibril, Umar Faruk. Kano, Nigeria: Center for Hausa Cultural Studies. 2004. ISBN 978-36906-0-4.OCLC 61158034.
Manazarta.
gyara sashe- ↑ Hausa home videos : technology, economy and society. Adamu, Abdalla Uba, 1956-, Adamu, Yusuf Muhammad., Jibril, Umar Faruk. Kano, Nigeria: Center for Hausa Cultural Studies. 2004. p. 2. ISBN 978-36906-0-4.
- ↑ Hausa home videos : technology, economy and society. Adamu, Abdalla Uba, 1956-, Adamu, Yusuf Muhammad., Jibril, Umar Faruk. Kano, Nigeria: Center for Hausa Cultural Studies. 2004.p. 7. ISBN 978-36906-0-4.
- ↑ Hausa home videos : technology, economy and society. Adamu, Abdalla Uba, 1956-, Adamu, Yusuf Muhammad., Jibril, Umar Faruk. Kano, Nigeria: Center for Hausa Cultural Studies. 2004.p. 7. ISBN 978-36906-0-4.
- ↑ Hausa home videos : technology, economy and society. Adamu, Abdalla Uba, 1956-, Adamu, Yusuf Muhammad., Jibril, Umar Faruk. Kano, Nigeria: Center for Hausa Cultural Studies. 2004.p. 7. ISBN 978-36906-0-4.
- ↑ Hausa home videos : technology, economy and society. Adamu, Abdalla Uba, 1956-, Adamu, Yusuf Muhammad., Jibril, Umar Faruk. Kano, Nigeria: Center for Hausa Cultural Studies. 2004.p. 8. ISBN 978-36906-0-4.
- ↑ Hausa home videos : technology, economy and society. Adamu, Abdalla Uba, 1956-, Adamu, Yusuf Muhammad., Jibril, Umar Faruk. Kano, Nigeria: Center for Hausa Cultural Studies. 2004.p. 9. ISBN 978-36906-0-4.
- ↑ Hausa home videos : technology, economy and society. Adamu, Abdalla Uba, 1956-, Adamu, Yusuf Muhammad., Jibril, Umar Faruk. Kano, Nigeria: Center for Hausa Cultural Studies. 2004. p. 10. ISBN 978-36906-0-4.
- ↑ Hausa home videos : technology, economy and society. Adamu, Abdalla Uba, 1956-, Adamu, Yusuf Muhammad., Jibril, Umar Faruk. Kano, Nigeria: Center for Hausa Cultural Studies. 2004.p. 11 ISBN 978-36906-0-4.
- ↑ 9.0 9.1 Hausa home videos : technology, economy and society. Adamu, Abdalla Uba, 1956-, Adamu, Yusuf Muhammad., Jibril, Umar Faruk. Kano, Nigeria: Center for Hausa Cultural Studies. 2004.p. 14.ISBN 978-36906-0-4.
- ↑ Hausa home videos : technology, economy and society. Adamu, Abdalla Uba, 1956-, Adamu, Yusuf Muhammad., Jibril, Umar Faruk. Kano, Nigeria: Center for Hausa Cultural Studies. 2004.p. 13-14. ISBN 978-36906-0-4.