Patrick Ikhariale
Patrick Ikhariale ɗan siyasar Najeriya ne wanda ya taɓa zama ɗan majalisar wakilai daga shekarun 2011 zuwa 2015, mai wakiltar mazaɓar tarayya ta Esan ta tsakiya/Esan West/Igueben a jihar Edo. [1]
Patrick Ikhariale | |
---|---|
Rayuwa | |
ƙasa | Najeriya |
Karatu | |
Harsuna | Turancin Birtaniya |
Sana'a | |
Sana'a | ɗan siyasa |
Imani | |
Jam'iyar siyasa | All Progressives Congress |
Tarihi da farkon rayuwarsa
gyara sashePatrick ɗan asalin Opoji ne a ƙaramar hukumar Esan ta tsakiya a jihar Edo a Najeriya. [2] [1] [3]
Aikin siyasa
gyara sasheAn zaɓi Ikhariale a matsayin ɗan majalisar wakilai ta 7 a shekarar 2011 a ƙarƙashin jam’iyyar PDP mai wakiltar mazaɓar Esan ta tsakiya Esan ta yamma/Igueben a jihar Edo, Najeriya. [1]
A lokacin da yake riƙe da muƙamin shugaban majalisar wakilai daga shekarar 2011 zuwa 2015, Patrick Ikhariale ya riƙe muƙamin shugaban kwamitin kula da wutar lantarki na majalisar. [4] [5] [6]
A watan Disambar 2013, Ikhariale, ya sauya sheka daga jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) zuwa jam’iyyar All Progressives Congress (APC). Bayan zamansa a majalisar wakilai a shekarar 2015, Ikhariale ya ci gaba da shiga jam'iyyar APC. A watan Fabrairun 2021, ya sake tabbatar da kasancewar sa a jam’iyyar. [7]
A shekarar 2023, an naɗa Ikhariale sakataren kwamitin mika mulki na jihar Edo karkashin Gwamna Monday Okpebolo. An ɗorawa kwamitin alhakin tabbatar da miƙa mulki cikin sauki daga gwamnatin mai barin gado zuwa sabuwar gwamnati. [8]
Ikhariale ya kuma taɓa zama sakataren kwamitin tantance kadarorin mutum 14 da gwamna Okpebholo ya kafa domin binciken gwamnatin gwamnan jihar Edo mai barin gado, Godwin Obaseki. Ayyukan kwamitin sun haɗa da tabbatar da kadarorin jihar da bayar da shawarwari don gudanar da ingantaccen shugabanci. [9] [10]
Manazarta
gyara sashe- ↑ 1.0 1.1 1.2 "Citizen Science Nigeria". citizensciencenigeria.org (in Turanci). Retrieved 2025-01-02. Cite error: Invalid
<ref>
tag; name ":0" defined multiple times with different content - ↑ Adesuwa Tsan and, Edegbe Odemwingie (April 30, 2012). "Nigeria: Privatisation of Power Sector, Only Way Out - Hon. Ikhariale". AllAfrica.
- ↑ "National Assembly | Federal Republic of Nigeria". 2015-10-02. Archived from the original on 2 October 2015. Retrieved 2025-01-02.
- ↑ "House Committee Urges DISCOs To Patronise Local Meters". :::...The Tide News Online:::... (in Turanci). 2014-06-20. Retrieved 2025-01-02.
- ↑ sweetcrudemain (2012-10-14). "Reps Committee commends Enugu Electricity Distribution Company". SweetCrudeReports (in Turanci). Retrieved 2025-01-02.
- ↑ ":: The Nigeria Electricity System Operator". www.nsong.org. Retrieved 2025-01-02.
- ↑ Jeremiah, Urowayino (2019-11-17). "EDO APC CRISIS:Why we moved against Obaseki —Ex-Rep, Ikhariale". Vanguard News (in Turanci). Retrieved 2025-01-02.
- ↑ Abdullah, Abdulsalam (2024-10-23). "Okpebholo's transition committee adjourns indefinitely over 'absence of vital documents'". TheCable (in Turanci). Retrieved 2025-01-02.
- ↑ "Gov Okpebholo constitutes 14-man panel to probe Obaseki – Nigerian Observer". nigerianobservernews.com (in Turanci). Retrieved 2025-01-02.
- ↑ Benin, Bisi Olaniyi (2024-11-25). "Okpebholo, Obaseki clash over move to probe past administration". The Nation Newspaper (in Turanci). Retrieved 2025-01-02.