Patrick Asadu
Patrick Asadu an haife shi a ranar 23 ga Agusta 1964 ɗan siyasar Najeriya ne kuma ƙwararren likita wanda ya fito daga Ovoko a cikin ƙaramar hukumar Igbo-eze ta Kudu a jihar Enugu wanda ke wakiltar mazabar Nsukka/Igbo-eze ta kudu a majalisar tarayyar Wakilai. An naɗa shi mai girma kwamishinan jihar Enugu bayan ya koma jam’iyyar PDP.[1]
Patrick Asadu | |||||||||
---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|
ga Yuni, 2019 - District: Nsukka/Igbo-Eze South
9 ga Yuni, 2015 - 9 ga Yuni, 2019 District: Nsukka/Igbo-Eze South
6 ga Yuni, 2011 - 6 ga Yuni, 2015 District: Nsukka/Igbo-Eze South
5 ga Yuni, 2007 - 6 ga Yuni, 2011 District: Nsukka/Igbo-Eze South | |||||||||
Rayuwa | |||||||||
Haihuwa | 23 ga Augusta, 1964 (60 shekaru) | ||||||||
ƙasa | Najeriya | ||||||||
Karatu | |||||||||
Harsuna |
Turanci Pidgin na Najeriya | ||||||||
Sana'a | |||||||||
Sana'a | ɗan siyasa | ||||||||
Imani | |||||||||
Jam'iyar siyasa | Peoples Democratic Party |
Rayuwar farko da karatu
gyara sasheAn haifi Asadu ga iyalan Pa David Ezenwa Asadu da kuma matar gidan, Mary Oriefi Asadu (nee Eze-Okwechi), duka sun rasu. Ya halarci Makarantar Sakandare ta Boy's Woko, kuma a 1982 ya ci jarrabawar West African Examination Council (WASC) da bambanci. Asadu yayi karatun likitanci da aikin tiyata a jami'ar Nigeria dake Nsukka kuma ya kammala karatun MBBS a 1988. Ya kuma samu digirin digirgir a fannin kiwon lafiyar jama'a a jami'ar Najeriya dake Nsukka. Asadu ya yi aiki a matsayin likita a ɓangaren gwamnati da masu zaman kansu. Asadu yayi aure.[2]
Naɗin siyasa
gyara sasheAsadu ya riƙe muƙamin siyasa da dama, waɗanda suka haɗa da:
- Hon. Kwamishinan Kimiyya da Fasaha, Jihar Enugu - 2001[3]
- Hon. Kwamishinan Filaye da Gidaje, Jihar Enugu 2000-2001
- Hon. Kwamishinan lafiya na jihar Enugu 2001-2002
- Shugaban kwamitin rikon kwarya na karamar hukumar Igbo-Eze ta Kudu 2002-2003
- Hon. Kwamishinan Noma na Jihar Enugu 2003-2005
- Hon. Kwamishinan Muhalli na Jihar Enugu 2005-2006
Manazarta
gyara sashe- ↑ https://www.manpower.com.ng/people/16767/hon-patrick-asadu
- ↑ "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2022-09-23. Retrieved 2023-03-11.
- ↑ https://nass.gov.ng/mps/single/242