Oulimata Sarr
Oulimata Sarr da aka haifa a Dakar a halin yanzu ita ce Darakta a yankin mata na Majalisar Dinkin Duniya mai kula da kasashe 24 na yammacin Afirka da tsakiyar Afirka.[1] Matan Majalisar Dinkin Duniya shine Majalisar Dinkin Duniya da aka wajabta don daidaiton jinsi da karfafawa mata.
Oulimata Sarr | |||
---|---|---|---|
17 Satumba 2022 - 11 Oktoba 2023 ← Amadou Hott (en) | |||
Rayuwa | |||
Haihuwa | Dakar, | ||
ƙasa | Senegal | ||
Karatu | |||
Makaranta |
HEC Montréal (en) University of Bedfordshire (en) | ||
Sana'a | |||
Sana'a | ɗan siyasa | ||
Employers |
Ernst & Young (en) Majalisar Ɗinkin Duniya International Finance Corporation (en) Government of Senegal (en) |
Farkon rayuwa
gyara sasheSarr ta girma a Senegal amma tayi karatu a Montréal, Kanada. Ta sauke karatu daga École des Hautes études Commerciales de Montréal (HEC Montréal) tare da digiri na farko a 1992, kuma bayan wani lokaci na kara karatu a Jami'ar Bedfordshire a Biritaniya, tayi karatu akan Master of Business Administration a 2002.
Ayyuka da Muƙamai
gyara sasheSarr ta shafe shekaru goma a Ƙungiyar Kuɗi ta Duniya, memba ta Ƙungiyar Bankin Duniya, kafin ta shiga Majalisar Dinkin Duniya.[2] Ta kuma yi aiki a matsayin babbar Auditor tare da Ernst & Young Senegal.
A cikin 2017, Vital Voices ta gayyace ta don shiga cikin Shirin Jakadun Duniya a matsayin mai ba da shawara ga mata 'yan kasuwa a duniya.Kwanan nan ta shiga cikin mata 75 na Afirka a matsayin memba ta kafa kungiyar saka hannun jari ta mata ta Senegal wacce aka kafa a cikin 2016 don samar da jari na dogon lokaci ga mata masu kasuwanci a Senegal.
Daga 1993 zuwa 2005, ta yi aiki a matsayin Babban Jami'in Harkokin Kuɗaɗe (CFO) na jirgin saman Afirka ta Kudu mai suna Interair South Africa.
Sarr ita ce shugabar (Jury) na gasar Cartier Women's Initiative Awards don Afirka kudu da kasashen yankin Sahara.[3]
A ranar 17 ga Satumba, 2022, ta zama ministar tattalin arziki, tsare-tsare da hadin gwiwa, a cikin gwamnatin Ba. Wannan shi ne karo na farko a Senegal da mace ta rike wannan mukamin minista.
Manazarta
gyara sashe- ↑ UN, Women. "UN women". UN Women.
- ↑ International, International Finance Corporation. "Senior Operation Officer".
- ↑ Cartier, Cartier Women's Initiative Awards. "Member of Jury".