Obi Iyiegbu
Obi Iyiegbu wanda aka fi sani da Obi Cubana (an haife shi ranar 12 ga watan Afrilu 1975). Dan kasuwa ne, ɗan Najeriya kuma ɗan kasuwa wanda ke shugabantar ƙungiyar Obi Obi Cubana.[1]
Obi Iyiegbu | |
---|---|
Rayuwa | |
Cikakken suna | Iyiegbu Obinna Tochukwu |
Haihuwa | Idemili ta Kudu, 12 ga Afirilu, 1975 (49 shekaru) |
ƙasa | Najeriya |
Harshen uwa | Harshen, Ibo |
Ƴan uwa | |
Mahaifiya | Ezinne |
Abokiyar zama | Ebele (mul) |
Karatu | |
Makaranta | University of Nigeria, Ozara-Ituku. Enugu State (en) |
Harsuna |
Turanci Harshen, Ibo Pidgin na Najeriya |
Sana'a | |
Sana'a | ɗan kasuwa |
Nauyi | 154.32 lb |
Imani | |
Addini | Kiristanci |
Farkon rayuwa
gyara sasheAn haifi Iyiegbu a ranar 12 ga Afrilu 1975 a Anambra kuma mahaifiyarsa ita ce Ezinne Iyiegbu. Ya fito ne daga Oba a karamar hukumar Idemili ta kudu a jihar Anambra .
Sana'a
gyara sasheAyyukan Iyiegbu a matsayin ɗan kasuwa ya fara ne a 2006 lokacin da ya kafa wani kulob na dare mai suna Ibiza Club a Abuja. A shekarar 2009, ya kafa kulob mai karban baki mai suna Cubana a Owerri, jihar Imo .[2]
Ilimi
gyara sasheYa fara karatunsa a Makarantar Firamare ta tsakiya kafin ya halarci Makarantar Grammar Memorial ta Dennis don karatun sakandare. Bayan kammala karatun sakandare, ya zarce zuwa jami’ar Najeriya Nsukka inda ya kammala da digirinsa na farko a fannin kimiyyar siyasa a shekarar 1998.[3]