Olugbemiro Jegede, Dan kasar Nageriya ne farfesa emeritus,a banagaren karantar da kimiyya, she ne wanda ya fara zama shugaban budaddiyar jami'ar najeria. kuma shine babban sakatare na baya na kungiyar jami'o'in Afrika kuma shine kansila. na jami'ar Littoral dake Porto-Novo, Jamhuriyar Benin[1][2][3][4]

Yayi digiri dinsa na farko dana biyu daga jami'ar Ahmadu Bello dage Zaria, a Najeriya kuma yayi digrin digirgir daga Kwalejin Jami'ar Wales, Cardiff, UK[5]

Olugbemiro Jegede ya fara aikin ilimi a matsayin malamin kimiyya a Makarantar Soja ta Najeriya,da ke Zaria a shekarar 1977. A shekarar 1974, ya zama mataimakin mai bincike na Sashen Ilimi, Jami’ar Ahmadu Bello, Zariya. Ya zama Mataimakin wanda ya kammala karatun digiri a Sashen Ilimi na Cibiyar a shekarar 1977, malamin jami'a mai mataki na 2 a shekarar 1979. malamin jami'a mai mataki na 1 a shekarar 1981. babban malamin jami'a a shekarar 1984 sai kuma mataimakin Farfesa a shekarar 1987[5]

Mataimakin Shugaban Jami’ar Budaddiyar Jami’ar Najeriya wanda ya kafata shine Farfesa Olugbemiro Jegede. Bayan ya kasance Ya kasance mai muhimmanci a Najeriya kan aiki na musamman a fannin ilimi, an nada shi Sakatare-Janar kuma Shugaban Kungiyar Jami'o'in Afirka a ranar 1 ga watan Disambar, 2010. Ya kuma kasance tsohon sakataren gwamnatin jihar Kogi. An nada Farfesa Olugbemiro Jegede a matsayin wanda ya assasa kuma a halin yanzu mataimakin shugaban Budaddiyar Jami’ar Nijeriya (NOUN) a shekarar 2003 bayan ya amsa goron gayyatar da gwamnatin tarayyar Najeriya ta yi masa na ci gaba da gudanar da ayyukan koyo na buda-baki da na nesa a kasar. A cikin 2001, ya ɗauki matsayin mai kula da shirye-shiryen koyan buɗaɗɗe da nisa na ƙasa.

Kyaututtuka da karramawa

gyara sashe

A shekarar 2015 ya karbi lambar yabo ta girmamawa daga Majalisar kasa da kasa don Budaddiyar Ilimi da Nisa (ICDE) a taron duniya na ICDE na 26th. (ICDE) a taron ICDE na 26th[6]. A cikin shekarar 2023, an kuma ba shi lambar yabo ta Ƙungiyar Jami'o'in Afirka (AAU) Babban Jakadan don Bude da Koyon Nisa a Afirka.[7]

Manazarta

gyara sashe
  1. "Future of Nigeria Private sector lies with Private Universities".
  2. "NOUN confirmed Olugbemiro Jegede as Professor Emeritus, and graduates 10,653". AAU Blog (in Turanci). 2016-01-21. Retrieved 2023-12-07.
  3. "PRIMATE NDUKUBA APPOINTS PROFESSOR OLUGBEMIRO JEGEDE AS HIS EDUCATION MATTERS ADVISER | Church of Nigeria (Anglican Communion)" (in Turanci). 2023-08-25. Retrieved 2023-12-07.
  4. FULokoja. ".:: FUL VC Felicitates Prof. Olugbemiro Jegede on Appointment as Chancellor, Littoral University, Porto-Novo, Republic of Benin | Federal University Lokoja". fulokoja.edu.ng (in Turanci). Retrieved 2023-12-07.
  5. 5.0 5.1 Andrew Aondofa, Chila. "Prof Olugbemiro Jegede: The ABU Alumnus Who Setup the National Open University of Nigeria".
  6. "Professor Olugbemiro Jegede receives Prize of Excellence". AAU Blog (in Turanci). 2015-10-22. Retrieved 2023-12-07.
  7. "Obasanjo speaks on Jegede's AAU award".