Niyyah
Niyyah (Larabci: نِيَّةٌ, fassarar daban-daban niyyah, niyya ar, "Niyya") Musulunci ne ya tsara haka: yin niyya a cikin zuciyar mutum don yin wani aiki na Ibadah don Allah ( Allah ).
Niyyah | |
---|---|
Islamic term (en) da Sufi terminology (en) | |
Bayanai | |
Ƙaramin ɓangare na | niyya |
Addini | Musulunci da Sufiyya |
Muhimmin darasi | Mubah (en) , batil (en) da Kabira (en) |
Mabiyi | Taklif (en) da will (en) |
Ta biyo baya | bauta a musulunci, aiki a musulunci, kyawawan aiki a musulunci, aiki da aiki |
Commemorates (en) | Volition of God in Islam (en) |
Depicts (en) | sincerity in Islam (en) da riya (en) |
Ta jiki ma'amala da | Noor (en) , Secret in Sufism (en) , Khafi (en) , Akhfa (en) da Ruh (en) |
Full work available at URL (en) | corpus.quran.com… da qurananalysis.com… |
Abu mai amfani | 'Aql (en) da Nafs (en) |
Shar'anta/wajabcin niyyah a Musulunci ya tabbata ne a cikin Alqur'ani mai girma cikin Surah ta 33 (Suratu Al-Ahzab) Aya ta 5:
Babu laifi a cikin abinda kuka aikata a bisa kuskure, face abinda kuka aikata da niyyah. Kuma Allah shine mai gafara mafi jinƙai.
Kamar yadda Ibn Rajab ya rawaito hadisi a cikin Arba’una Hadis na Imamu Nawawi: Hadisi na 1, ana hukuncin ayyuka ne da niyya: “ Umar b. al-Khattab ya ruwaito cewa, Annabi ya ce: Lallai tabbas dukkan Ayyuka sai da niyya, kuma mutum yana samun lada ne kawai bisa ga abin da ya yi niyya." [1]
Hakazalika, niyyar mutum na da matuqar muhimmanci a cikin sharuɗɗan layya. Akwai muhawara dangane da wajabcin yin lafazin yayin Niyyah. Mafi yawan malamai sun yarda cewa, duk niyyah ana qudurta ta a zuciya ne, ba sai an furta ta ba a baki. Bugu da ƙari, babu wata shaida da ke nuna cewa Annabin Musulunci Muhammad (S A W) ko wani daga cikin sahabbansa sun taɓa yin niyya da a bayyane kafin salla.
Dole ne musulmi ya kasance ya ƙulla niyya kafin ya fara sallah, da kuma fara aikin Hajji a ( Makka ).
Duba kuma
gyara sasheManazarta
gyara sashe- ↑ "Commentary: Hadith "Deeds are by Intentions"". sunnah.org. Archived from the original on February 23, 2020. Retrieved 2021-06-11.