Nasiru Idris
Mohammed Nasir Idris (an haife shi 6 ga Agusta[ana buƙatar hujja]1965) ne, ƙwararren ilimi, ɗan siyasa wanda yake rike da mukamin gwamnan jihar Kebbi a halin yanzu. A baya ya taba zama shugaban kungiyar malamai ta Najeriya kuma mataimakin shugaban kungiyar kwadago ta Najeriya.[1] A ranar 17 ga Afrilu, 2023, hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta bayyana Idris a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar Kebbi a shekarar 2023.[2][3]
Nasiru Idris | |||
---|---|---|---|
2023 - | |||
Rayuwa | |||
Haihuwa | Birnin, Kebbi, 6 ga Augusta, 1965 (59 shekaru) | ||
ƙasa | Najeriya | ||
Karatu | |||
Makaranta | Jami'ar Usmanu Danfodiyo | ||
Harsuna |
Hausa Turanci Pidgin na Najeriya | ||
Sana'a | |||
Sana'a | ɗan siyasa da trade unionist (en) | ||
Imani | |||
Addini | Musulunci | ||
Jam'iyar siyasa | All Progressives Congress |
Rayuwar farko da ilimi
gyara sasheAn haifi Nasir Idris a ranar 6 ga watan Agusta[ana buƙatar hujja] ƙaramar hukumar Birnin Kebbi a jihar Kebbi.[4] Ya halarci Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Birnin Kebbi tsakanin shekarar 1994 zuwa 2003, da Jami'ar Usmanu Danfodio, Sokoto, tsakanin 2006 zuwa 2009 don yin MBA. [4] Idris ya yi digirin digirgir a fannin ilimi kuma ya rubuta kasidu daban-daban kan ilimi.[5]
Sana'a
gyara sasheA shekarar 2018, an zaɓi Idris a matsayin shugaban kungiyar malamai ta Najeriya (NUT) da kuma mataimakin shugaban kungiyar kwadago ta Najeriya NLC.[6] Tsohon shugaban kungiyar NUT reshen jihar Kebbi, tsohon shugaban NLC, jihar Kebbi kuma tsohon ma'ajin kungiyar NUT ta kasa.[7] A watan Mayun 2022, Mista Idris ya fito a matsayin dan takarar gwamna na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na jihar Kebbi a zaben fidda gwani na gwamnan APC.[8] A ranar 17 ga Afrilu, 2023, Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta ayyana Idris a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar Kebbi a shekarar 2023.[9]
Nassoshi
gyara sashe- ↑ Sub-editor (2023-04-17). "Meet Dr Nasiru Idris, winner of Kebbi State Governorship Election". NewsWireNGR (in Turanci). Retrieved 2023-04-22.
- ↑ "Kebbi poll: INEC declares APC guber candidate, Nasir Idris, winner". Punch Newspapers (in Turanci). 2023-04-17. Retrieved 2023-04-22.
- ↑ "My Top Priority is education sector in Kebbi – Governor Elect Dr. Nasir Idris - INDEPENDENT POST NIGERIA" (in Turanci). 2023-04-17. Retrieved 2023-04-22.
- ↑ 4.0 4.1 "Decision Day 2023: Those who will be governors". The Sun News Online.
- ↑ "Seven things to know about Kebbi gov-elect, Idris". Punch Newspapers (in Turanci). 2023-04-16. Retrieved 2023-04-22.
- ↑ Rapheal (2019-05-07). nut-president/ "It's wickedness to pay primary school teachers salary in percentage, says Nasir, NUT President" Check
|url=
value (help). The Sun Nigeria (in Turanci). Retrieved 2023-04-22. - ↑ "NUT National President, Nasir Idris emerges Kebbi APC Guber candidate – Nigeria News" (in Turanci). Retrieved 2023-04-22.
- ↑ "NUT National President, Nasir Idris emerges Kebbi APC Guber candidate – Nigeria News" (in Turanci). Retrieved 2023-04-22.
- ↑ "APC's Nasiru Idris Wins Kebbi Governorship Poll – THISDAYLIVE". www.thisdaylive.com. Retrieved 2023-04-22.