Mutanen Bakulu
Mutanen Bakulu (kuma Ikolu, Ikulu, Bekulu) mutane ne da aka samo su a cikin Zangon Kataf, Kachia da Kauru ƙananan hukumomin da ke kudancin jihar Kaduna ta (Tsakiya) Najeriya . Suna jin yaren Filato da ake kira Kulu . Suna kiran ƙasarsu Akulu.[1]
Yankuna masu yawan jama'a | |
---|---|
Najeriya | |
Harsuna | |
Kulu (en) |
Jimlar yawan jama'a | |
---|---|
50,000 (1998)[1] | |
Yankuna masu yawan jama'a | |
Nigeria | |
Harsuna | |
Kulu | |
Addini | |
African Traditional Religion, Islam, Christianity | |
Kabilu masu alaƙa | |
Adara, Anghan, Bajju, Atyap, Ham, Tarok, Jukun, Efik, Igbo, Yoruba and other Benue-Congo peoples of Middle Belt and southern Nigeria |
Addini
gyara sasheYawancin mutanen Bakulu sun kuma kasance masu bin addinin gargajiya, wanda yawansu ya kai kusan 29.5% na yawan jama'ar, yayin da kuma Musulmai suka kai kashi 0.5% sannan Kiristoci da kashi 70.0% na jama'ar. Daga cikin Kiristocin, Masu zaman kansu suna da 60.0%, Furotesta 25.0% da Roman Katolika 15.0%.[2]
Siyasa
gyara sasheAna kuma kiran babban mai mulkin mutanen Bakulu da "Agwom" (ko Agom). Sarkin da yake yanzu shine Mai martaba (HRH) Agwom Yohanna Sidi Kukah, Agwom Akulu II . Agwom Akulu shine shugaban majalisar gargajiya ta Akulu na masarautar Akulu (Ikulu), wanda cibiyarsa take a Faɗan Ikulu a Kamuru.[3][4]
Ƙananan yankuna
gyara sasheAn kuma san ƙasar mutanen Bakulu da suna Akulu ( Hausa: Ikulu). Ikulu na daya daga cikin kananan hukumomi 11 na ƙaramar hukumar Zangon Kataf da ke kudancin jihar Kaduna . Hakanan an raba shi zuwa:
- Gidan Pate
- Gidan Zomo
- Kamaru Ikulu ( Kamuru )
- Kamaru Hausawa (Kamuru)
- Katul
- Ungwan Jada
- Ungwan Jatau
- Ungwan Pa
- Ungwan Sani
- Yadai
Wani fitaccen dan Bakulu, Rev. Fr. Matthew Kukah ya yanke hukunci a wata hira da yayi da jaridar This Day News cewa Bakulu tare da Anghan sune kananan kungiyoyi a karamar hukumar tare da kowannensu yana da yanki kawai duk da kuma yawansu.
Sananne mutane
gyara sashe- Bishop Matthew Hassan Kukah, Bishop na Roman Katolika Diocese na Sokoto
Manazarta
gyara sashe- ↑ 1.0 1.1 "Ikulu". Ethnologue. Retrieved 2017-04-30.
- ↑ "Glottolog 3.0 -Ikulu". glottolog.org (in Turanci). Retrieved 2017-04-30.
- ↑ "Fadan Ikulu/Kaduna State". Retrieved August 8, 2020.
- ↑ "Kamaru Ikulu Map - Satellite Images of Kamaru Ikulu". Retrieved August 8, 2020.